Gwamna Radda Ya ba Dalibin da Ya Gama Jami'a da Sakamako Mafi Kyau Yana Tallan Ruwa Aiki
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya shiga lamarin dalibin da ya kammala jami'a da daraja ta daya, amma ya fara tallan ruwan leda
- Dalibin mai suna Sham'unu Ishaq ya kammala karatu ne a jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke jihar Katsina a zangon 2021/2022
- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ta yi bincike a jami'ar domin tabbatar da cewa Sham'unu Ishaq ya kammala makarantar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya gwangwaje dalibin da ya kammala jami'a ya fara tallan ruwan leda.
An ruwaito cewa dalibin mai suna Sham'unu Ishaq ya kammala karatun jami'a da daraja ta daya amma ya fara talla saboda rashin aikin yi.
Hadimin Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayyana matakin da gwamnatin Katsina ta dauka a wani sako da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hazikin dalibin Katsina ya samu aiki
A ƴan kwanakin nan aka rika yada bidiyon wani matashi dan jihar Katsina da ya kammala jami'a da daraja ta daya ya fara tallan ruwan leda.
Lamarin ya jawo hankalin gwamnatin Katsina yin bincike a jami'ar Umaru Musa Yar'adua a kan gaskiyar karatun tsohon dalibin.
Bayan tabbatar da labarin, Gwamna Dikko Umaru Radda ya ba Sham'unu Ishaq aiki domin ya samu abin yi.
"Mun tabbatar da cewa ya kammala jami'ar Umaru Musa Yar'adua a shekarar 2021/2022.
Akwai bukatar karfafa dalibai masu ƙoƙari kuma bai kamata a bar wanda ya gama jami'a da daraja ta daya yana talla a kan titi ba.
Gwamna Radda ya umarci da a ba Sham'unu Ishaq aiki nan take ta hannun shugaban ma'aikata."
- Gwamnatin Katsina
Gwamna Radda ya bayyana cewa hakan na cikin kokarinsa na bunƙasa ilimi a jihar Katsina kuma ba wannan ke karon farko da ya ba dalibai masu hazaka aiki ba.
Dikko Radda zai kashe N20bn kan ruwa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda ta ware N20bn domin gudanar da aikin samar da ruwa a faɗin jihar.
Kwamishinan albarkatun ruwa, Dr. Bashir Gambo Saulawa ya ce aikin zai gudana ne karkashin shirin SURWASH na bankin duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng