"Da Yanzu Dala Ta Kai N10,000" Malami Ya Faɗi Taimakon da Allah Ya Yi Wa Najeriya
- Jagoaran cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa babu abin da Najeriya ta fi bukata a yanzu kamar addu'a
- Da yake jawabi a wani taro a Abuja, Malamin cocin ya ce ba don taimakon Allah ba da yanzun canjin Dala ya kai N10,000
- Fasto Adeboye ya kuma soki tsohuwar gwamnati bisa kashe biliyoyin Naira kan matatun man da ba su aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya ce ba don taimakon Allah ba, da yanzun canjin Naira ya kai N10,000/1$.
Malamin cocin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin wani taron addinin kirista a birnin tarayya Abuja.
Malamin coci ya faɗi tushen matsalar Najeriya
Adeboye ya danganta matsalar da Najeriya ke fama da ita da dogaro da shigo da mai daga kasashen waje, duk da kasancewarta kasa mai albarkatun mai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Nation ta ce Faston ya kuma soki biliyoyin da aka kashe kan matatun da ba su aiki, lamarin da ya tilasta wa kasar dogaro da man da ake shigowa da shi daga ƙetare.
Da yake tsokaci kan takaddamar cire tallafin man fetur, Adeboye ya ce tuge tallafin ya fusata wadanda ke cin moriyar da tsarin da aka baro.
Fasto Adeboye ya kara jaddada cewa Najeriya na bukatar addu'a domin samun taimakon Allah ba na wani ɗan adam ba, rahoton Daily Post.
"Da yanzu Dala ta kai N10,000" - Adeboye
"Kafin shugaban ƙasa mai ci ya hau kan madafun iko, kowa ya san babbar matsalar da ta addabi Najeriya ita ce shigo da man fetur daga ƙasshen ƙetare.
"Haka muka ci gaba da shigo da man fetur tare da kashe maƙudan kudi a kan matatun man da har yanzun ko ɗaya ta kasa tashi.
"Ba don Allah ya kawo mana ɗauki ba, da yanzu kowace Dala ɗaya ta kai N10,000, wannan yana nuna babu abin da muke bukata kamar addu'a."
- Fasto Adeboye.
Matsin rayuwa: Tinubu ya ba ƴan Najeriya hakuri
A wani labarin, an ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya da su kara hakuri kan halin wahalar rayuwa da suke ciki a halin yanzu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa da sannu za a samu sauki a kan halin da ake ciki a tarayyar Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng