Gwamna a Arewa Ya Kinkimo Aikin da Zai Laƙume Naira Biliyan 20
- Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda ta ware N20bn domin gudanar da aikin samar da ruwa a faɗin jihar
- Kwamishinan albarkatun ruwa, Dr. Bashir Gambo Saulawa ya ce aikin zai gudana ne karkashin shirin SURWASH na bankin duniya
- A cewar gwamnatin Radda, za a fara aikin ne a yankunan ƙananan hukumomi 10 sannan a faɗaɗa shi zuwa wasu garuruwa a 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Raɗɗa ta ware Naira Biliyan 20 domin gudanar da aikin samar da tsaftataccen ruwa.
Wannan aiki da gwamnatin Radda ta kinkimo wani bangare ne na shirin samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a Nijeriya (SURWASH) da bankin duniya ke tallafawa.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shirin ya ƙunshi fadada hanyoyin samar da ruwa mai tsafta ga al'umma da tabbatar da tsaftar muhalli a fadin jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan albarkatun ruwa, Dr Bashir Gambo Saulawa, ya tabbatar da yunƙurin gwamnatin Katsina na fitar da waɗannan kuɗi domin aikin ruwa.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya fitar da N5bn
Da yake zantawa da manema labarai, Dr. Bashir Saulawa ya ce tuni gwamna ya amince da fitar da Naira biliyan 5 domin fara aikin gadan-gadan.
"Tsarin aikin zai fara ne daga kananan hukumomi 10 a shekarar 2024, sannan za a faɗaɗa shi zuwa wasu yankunan a 2025," in ji shi.
Abin da aikin ruwan Katsina ya ƙunsa
Babban daraktan hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Katsina (RUWASSA), Suleiman Abukur, ya bayyana takamaiman manufofin aikin.
Ya ce za a fara aikin da garuruwa 110 na kananam hukumomi takwas da suka haɗa da Charanchi, Batagarawa, Baure, Daura, Funtua, Malumfashi, Kafur da Kankara.
"Muna shirin tona rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana 40 a a kauyuka 40 tare da gyara wasu rijiyoyin burtsatse a wasu garuruwa 50," in ji shi.
Wani manomi kuma ma'aikacin gwamnati a Katsina, Malam Abdullahi Sule ya yi maraba da wannan aikin, wanda a cewarsa zau bunkasa harkokin noma.
Ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa gwamnatin Katsina ta jima tana zancen wannan aikin to amma yana fatan wannan karon ya zana an fara aiwatarwa.
"Ba yanzu aka fara batun aikin samar da ruwan nan ba, a baya na samu labarin za a gyara mana madatsun ruwa, ƙarisa wadanda aka fara da ma kirkiro wasu.
"Wannan zai taimake mu saboda noman rani kuma ita kanta gwamnati za ta ƙara samun kuɗaɗen shiga, muna fatan Allah ya sa a yi wannan aikin," in ji Abdullahi.
Gwamnan Katsina ya fara gyaran asibitoci
Ku na da labarin gwamna Dikko Radda ya kara ba da umarnin sabunta ƙananun asibitoci 34 tare ɗaga darajarsu a faɗin jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne a lokacin da aikin gyaran asibitocin gwamnati sama da 100 ya yi nisa a faɗin ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng