Tsohon Gwamna Ya Shiga Matsala kan Zargin 'Satar' N1.3trn, An Haramta Masa Fita Najeriya

Tsohon Gwamna Ya Shiga Matsala kan Zargin 'Satar' N1.3trn, An Haramta Masa Fita Najeriya

  • Hukumar EFCC ta karɓe fasfon tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa gabanin ta amince da bada belinsa
  • Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun cafke Okowa ne bisa zargin karkatar da kudi da yake mulkin Delta
  • Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce karɓe farfon wanda ake zargi a matsayin sharadin beli ba sabon abu ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa watau EFCC ta haramta wa tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa fita zuwa ƙasashen ketare.

Hukumar EFCC ta hana Okowa yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ne bayan ta karɓe fasfo ɗinsa a sharuɗɗan ba da beli.

Ifeanyi Okowa.
Hukumar EFCC ta haramtawa tsohon gwamnan Delta fita Najeriya Hoto: Ifeanyi Okowa
Asali: Facebook

Hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa ta kama Okowa tare da tsare shi a makon da ya gabata bisa zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3, Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ondo: Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ɗan takarar gwamna kwanaki 2 gabanin zaɓe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a ranar Lahadin da ta shige, EFCC ta amince da sakin tsohon gwamnan a matsayin beli bisa wasu sharuɗɗa ciki har da ƙwace fasfo dinsa.

EFCC: Dalilin kama tsohon gwamnan Delta

Tun da fari EFCC ta gayyaci Okowa, tsohon dan takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2023 a inuwar PDP domin ya amsa tambayoyin kan zargin satar kudin talakawa.

Okowa ya amsa gayyatar EFCC ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, sai dai daga zuwa jami'ai suka yi ram da shi.

Ana zargin an kama tsohon gwamnan ne kan kashi 13% da ake warewa jihohin da ke yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Hukumar EFCC ta tabbatar da karɓe fasfon Okowa

Da aka tuntube shi don tabbatarwa, mai magana da yawun hukumar EFCC, Mista Dele Oyewale, ya ce al’adar hukumomin tabbatar da doka ne kwace fasfo kafin gama bincike.

"Wannan ba sabon abu ba ne, al'ada ce ta hukumomin tabbatar da doka, idan suka bayar da beli su karɓe fasfo da wasu takardu, ba sabon abu ba ne wannan."

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

Tsohon gwamnan Delta ya maida martani

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya musanta zargin karkatar da N1.3trn daga asusun jihar daga 2015-2023.

Sanata Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa bai da wani abin da zai ɓoye dangane da yadda ya ja ragamar mulkin jihar a tsawon shekara takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262