Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Hanyar Samun Wadatacciyar Wutar Lantarki a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana buƙatar maƙudan kuɗi domin samar da wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar nan
- Ministan makamashi ya bayyana cewa ana buƙatar zuba hannun jarin $10bn kafin a riƙa samun lantarki ta tsawon sa'o'i 24 a kullum
- Adebayo Adelabu ya nuna gwamnati ita kaɗai ba za ta iya yin hakan ba, inda ya buƙaci kamfanoni masu zaman kansu su so a haɗa kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana kuɗin da ake buƙata domin samun wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar nan.
Gwamnatin ta bayyana cewa tana buƙatar zuba jarin $10bn a fannin samar da wutar lantarki, nan da shekar biyar zuwa 10 masu zuwa, domin samar da haske na tsawon sa'o'i 24 a kullum.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana haka a lokacin da Darakta-janar na hukumar ICRC, Dr Jobson Ewalefoh, ya kai masa ziyara, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ba za ta iya samar da lantarki ba
Sanarwa kan ziyarar ta fito ne ta hannun Mista Ifeanyi Nwoko, muƙaddashin shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar ICRC a ranar Laraba a Abuja, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
A cikin sanarwar, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ita kaɗai, ba za ta iya samar da $10bn ba yayin da akwai wasu sassa masu muhimmanci suke buƙatar kuɗade.
"Gwamnati ba za ta iya yin hakan ita kaɗai ba, don haka dole ne mu nemi tallafin kamfanoni masu zaman kansu, yayin da gwamnati za ta ci gaba da riƙe wani kaso na ikon mallaka."
"A nan ne ya kamata ICRC ta shigo. Muna buƙatar yin hakan tare da haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu kuma hanya mafi kyau ita ce ta hanyar jingina."
- Adebayo Adelabu
EFCC ta gano matsalar lantarkin Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya danganta rashin wutar lantarki mai kyau a Najeriya da cin hanci a bangaren samar da wutar.
Ola Olukoyede ya ce 'yan Najeriya za su cika da mamaki idan har har aka bayyana sakamakon binciken da EFCC ta gudanar a fannin wutar ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng