Badakalar N1.3trn: Tsohon Gwamna Ya Yi Martani kan Gayyatar da EFCC Ta Yi Masa

Badakalar N1.3trn: Tsohon Gwamna Ya Yi Martani kan Gayyatar da EFCC Ta Yi Masa

  • Tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya musanta karkatar da N1.3trn daga asusun jihar lokacin da ya yi mulki daga 2015-2023
  • Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa bai da wani abin da zai ɓoye dangane da yadda ya ja ragamar mulkin jihar a tsawon shekara takwas
  • Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne dai bayan hukumar EFCC ta fara bincikensa kan zargin karkatar da kudaden jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Tsohon gwamnan Delta, Dakta Ifeanyi Okowa, ya yi martani kan zargin da hukumar EFCC ke yi masa na karkatar da kuɗin jihar.

Ifeanyi Okowa ya ce babu abin da zai boye dangane da tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulkin jihar.

Okowa ya yi martani kan gayyatar EFCC
Ifeanyi Okowa ya musanta karkatar da N1.3trn na jihar Delta Hoto: @OfficialEFCC, @IAOkowa
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Olisa Ifeajika ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya dauki muhimmin alkawari bayan rantsuwar kama aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okowa ya yi martani kan gayyatar EFCC

Ya bayyana cewa surutun da aka yi ta yi bayan yaje ofishin EFCC, wani yunƙuri ne da wasu ƴan siyasa ke yi a jihar domin shirin zaɓen 2027 da ke tafe, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Olisa Ifeajika ya bayyana cewa da yawa daga cikin matakan da Okowa ya ɗauka a lokacin da yake kan karagar mulki, sun samar da sakamako mai kyau wajen bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya bayyana cewa bayyanar tsohon gwamnan a ofishin EFCC alamu ne da ke nuna cewa ba shi da wani abin ɓoyewa dangane da yadda ya ja ragamar jihar a lokacin mulkinsa.

Tsohon gwamnan Delta ya karkatar da N1.3trn?

Hadimin ya ƙara da cewa zargin karkatar da N1.3trn da ake yi wa Okowa abu ne wanda hankali ba zai ɗauka ba.

"Shin ana so mu yarda cewa gwamnatin Okowa ba ta biya albashi ba, ko ba ta yi wani aiki ko guda ɗaya ba a cikin shekara takwas?"

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan tashin bam a babban birnin jihar Arewa

"Sai mutum ya riƙa ɗaukar N16bn kowane wata har tsawon shekara takwas sannan zai tattara zunzurutun kuɗi N1.3trn da ake zargin Okowa ya sace."

- Olisa Ifeajika

Gwamna ya tsorata kan binciken EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya tsorata da barazanar da hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ke yi masa.

Gwamnan ya fara ɗaukar matakin kariya inda ya garzaya kotu ya na neman a yi masa tsakani da jami’an hukumar EFCC idan wa’adinsa ya kare a matsayin gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng