Tankar Mai Ta Kara Kamawa da Wuta a Jigawa Kwanaki Bayan Rasa Rayuka a Majia

Tankar Mai Ta Kara Kamawa da Wuta a Jigawa Kwanaki Bayan Rasa Rayuka a Majia

  • Hukumar kashe gobara ta kasa reshen jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar hadarin tankar man fetur a safiyar ranar Talata
  • Rahotanni sun nuna cewa bayan samun kiran gaggawa, jami'an kashe gobara sun isa wajen kuma sun kashe wutar da ta kama
  • Kakakin hukumar kashe gobara ta kasa a Jigawa, Auwal Muhammad Abdullahi ta tabbatarwa Legit yadda hadarin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Rahotanni da suka fito daga jihar Jigawa na nuni da cewa an sake samun hadarin tankar man fetur.

Hukumar kashe gobara ta kasa reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa haɗarin bai jawo asarar rayuka ba.

Tankar mai
Tankar mai ta sake hadari a Jigawa. Hoto: Federal Fire Service Jigawa
Asali: UGC

Kakakin hukumar kashe gobara, Muhammad Abdullahi ya bayyanawa Legit yadda suka samu labarin hadarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sake hadarin tankar mai a Jigawa

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

Hukumar kashe gobara ta kasa ta tabbatar da sake samun hadarin tankar man fetur a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar, Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa a ranar Talata suka samu labarin hadarin kuma nan take suka tunkari wajen domin kai dauki.

"A ranar 12 ga watan Nuwamba muka samu kiran gaggawa daga sarkin ƙauyen Kuho, Zubairu Ahmad kan hadarin tankar mai.
Hadarin ya faru ne a yankin Tsaida, Kwanar Kalle a kusa da ƙauyen Gamoji.
Mun samu nasarar kashe wutar da ta kama kuma babu wanda ya rasa rai, sai dai mata daya ya ji karamin rauni."

- Hukumar kashe gobara

Bayanin kakakin yan sandan Jigawa

Kakakin yan sandan jihar Jigawa ya zantawa Legit cewa wayar da kan al'umma na cikin abubuwan da suka taimaka wajen nisantar wajen hadarin.

DSP Lawal Shiisu Adam ya ce babu wanda ya nufi wajen hadarin domin dibar man fetur ko kallon abin da ya faru.

Kara karanta wannan

An bayyana ɓangarorin da Saudiyya za ta yi haɗaka da Najeriya

APC ta yi jaje ga mutanen jihar Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna alhininsa kan iftila'in fashewar tankar maibda ya auku a Jigawa.

Abdullahi Ganduje ya yi wa gwamnati da al'ummar jihar Jigawa ta'aziyya kan rasuwar mutanen da aka samu sakamakon fashewar tankar man.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng