'Yan Bindiga Sun Karbe Matsayin Sarakuna a Jihar Arewa? An Gano Gaskiya
- Gwamnatin Kebbi ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ƴan bindiga sun karɓe ikon wasu ƙauyukan da ke jihar
- Mataimakin gwamnan jihar Kebbi ya bayyana cewa rahotannin tsantsagwaron ƙarya ne da babu ƙamshin gaskiya a ciki
- Sanata Umar Abubakar-Tafida ya bayyana cewa babu sansanin ƴan bindiga ko guda ɗaya a faɗin jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnatin Kebbi ta yi martani kan batun cewa ƴan bindiga sun karɓe ikon wasu ƙauyuka a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa babu wani ƙauye ɗaya da ke hannun ƴan bindiga inda suke saukewa tare da naɗa sarakunan gargajiya.
Mataimakin gwamnan jihar Umar Abubakar-Tafida, ya ƙaryata rahoton a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Umar Abubakar-Tafida ya bayyana cewa rahotannin da aka yaɗa kan karɓe ikon kotunan shari'ar musulunci da ƴan bindigan suka yi.
A cewarsa babu ƙamshin gaskiya a cikin labaran, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Babu wasu ƴan bindiga a jihar Kebbi
Mataimakin gwamnan ya ba da tabbacin cewa babu sansanin ƴan bindiga ko ɗaya a jihar Kebbi.
"Babu wani ƙauye guda ɗaya, a fadin jihar Kebbi, inda ƴan bindiga ke da iko kan kotunan shari’ar musuluncu ko kuma suke naɗa masu sarautun gargajiyan da suke so."
"Rahoton ƙarya ne, babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikinsa. Ba mu da sansanin ƴan bindiga a Kebbi."
"Waɗannan miyagun suna shigowa ne daga jihohi makwabta da jamhuriyar Nijar ta hanyar masu ba su bayanai su kai farmaki sannan su koma."
- Sen. Umar Abubakar-Tafida
Umar Abubakar-Tafida ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta samar da tsare-tsare masu kyauda za su kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci.
Gwamnan Kebbi ya yi ta'aziyya
A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu ya miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar kauyen Mera da ke ƙaramar hukumar Augie.
Gwamnan ya jajantawa mutanen garin sakamakon mummunan harin ƴan bindiga, wanda ake zargin sabuwar kungiyar ta'addanci ta Lakurawa ce ta kai harin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng