Wutar Lantarki: Asirin Yan Kwangila Ya Tonu, EFCC Ta Zarge Su da Jawo Matsala

Wutar Lantarki: Asirin Yan Kwangila Ya Tonu, EFCC Ta Zarge Su da Jawo Matsala

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta ce wasu yan kwangila sun taimaka wajen lalacewar wutar lantarki
  • Shugaban hukumar, Ola Olukayode ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi yan kwamitin yaki da rashawa na majalisar kasar nan
  • Ya bayyana cewa algus da wasu daga cikin yan kwangila su ka yi ya taimaka wajen matsalar wutar lantarki da ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaHukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta bayyana wanda ta ke zargi da hannu a jawo matsaloli a bangaren wutar lantarki.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ana zargin wasu gurbatattun yan kwangila da hannu a cikin yadda turakun wutar lantarki ke yawan faduwa a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano abubuwa 3 da suka jawo wutar lantarkin Najeriya ke yawan lalacewa

Lantarki
EFCC ta zargi yan kwangila da jawo matsala a bangaren lantarki Hoto: Economic and Financial Crimes Commission/TCN
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ruwaito cewa ana zargin wasu daga cikin yan kwangila da amfani da kayan aiki marasa inganci, wanda daga bisani su ke jawo matsalolin a bangaren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta gano wasu matsalolin wutar lantarki

Jaridar The Cable ta wallafa cewa hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa ta dora alhakin yawaitar matsalolin wutar lantarki a kan amfani da kaya marasa kyau.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka a hedikwatarsu da ke Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin yan kwamitin yaki da rashawa na majalisar dattawan kasar nan.

EFCC ta yi binciken matsalar wutar lantarki

EFCC ta bayyana sakamakon binciken da ta yi na dalilin yawaitar samun mastsala da ake yi a bangaren wutar lantarki.

Hukumar ta ce daga cikin abubuwan da ta gano, akwai yadda yan kwangila ke aikata rashin gaskiya a wajen aiki da gwamnati ke ba su.

Kara karanta wannan

Abuja ta fada cikin duhu, 'yan ta'adda sun lalata turken wayoyin wutar lantarki

Wutar lantarkin Abuja ya samu matsala

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan ta’adda sun kai hari kan wayoyin turakun wutar lantarki a hanyar Lokoja zuwa Gwagwalada, lamarin da ya sake jefa jama’ar Abuja a duhu.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya gano cewa yan ta’addan sun sace muhimman kayan amfanin wutar, su ka bukaci agajin mutane wajen dakile hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.