Rayukan Matasa Sun Salwanta bayan Ruftawar Mahakar Ma'adanai a Filato
- Wata mahakar ma'adanai ta sake ruftawa a Filato inda ta kashe wasu ma'aikata da dama a ƙaramar hukumar Bassa
- Mutane 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu a iftila'in da ya afku ranar 10 Nuwamba, 2024 a lokacin da su ke tsaka da aiki
- Shugaban karamar hukumar Bassa, Joshua Riti ya tabbatar da lamarin tare da mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - An tafka asarar rayuka a jihar Filato bayan wata mahakar ma'adanai ta rufta da ma'aikata a cikinta ana cikin aiki.
Mummunan lamarin ya afku ne a karamar hukumar Bassa inda mutane akalla 13 su ka rasa rayukansu a hadarin da ya gigita jama'a.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa shugaban karamar hukumar Bassa, Joshua Riti ya tabbatar da afkuwar ruftawar mahakar da asarar rayuka.
Mahakar ma'adanai ta rufta a Filato
Jaridar The Nation ta wallafa cewa wata mahakar ma'adanai da ke yankin Bassa ta kuma hada iyaka da kananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa ta rufta.
Lamarin ya ya afku a ranar 10 Nuwamba, 2024 ya kashe mutane akalla 13 da su ke neman abincinsu a yankin.
An yi ta'aziyyar wanda mahaka ta danne
Shugaban karamar hukumar Bassa, Joshua Riti ya mika ta'aziyya ga yan uwan wanda su ka rasa rayuwarsu a mahakar da ke yankin.
Ya bayyana takaici bisa yadda mahakar ta danne bayin Allah da ke amfani da karfinsu wajen neman halak dinsu domin samun saukin matsin rayuwa.
Mahakar ma'adanai ta rufta a Neja
A baya mun wallafa cewa wasu mutane sun rasa rayukansu bayan mahakar ma'adanai ta rufta a jihar Neja, jim kadan bayan mutuwar mutum 20 a irin hadarin.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) Alhaji Abdullahi Baba-Arah da ya tabbatar da iftila'in ya ce mutane uku ne su ka koma ga mahaliccinsu a lokacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng