Gwamnan Edo Ya Dauki Muhimmin Alkawari bayan Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki

Gwamnan Edo Ya Dauki Muhimmin Alkawari bayan Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki

  • Sabon gwamnan jihar Edo wanda ya kama rantsuwar aiki a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba ya ɗauki alƙawari ga mutanen da zai jagoranta
  • Gwamna Monday Okpebholo ya yi alƙwarin cewa da shi da mataimakinsa ba za su ci amanar nauyin da aka ɗora musu ba
  • Mai girma Gwamnan ya bayyana cewa zai maida hankali wajen bunƙasa tattalin arziƙi da jin daɗin mutanen jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - A ranar Talata aka rantsar da Sanata Monday Okpebolo da Dennis Idahosa a matsayin gwamna da mataimakin gwamnan jihar Edo.

Babban alƙalin jihar, mai Shari’a Daniel Okungbowa, shi ne wanda ya jagoranci rantsar da Okpebolo da Idahosa domin fara jan ragamar mulkin Edo.

An rantsar da gwamnan Edo
Gwamna Okpebholo ya ce ba zai ci amanar mutanen Edo ba Hoto: @Okpebholoupdates
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa rantsar da Sanata Okpebolo ta sanya ya zama gwamnan farar hula na shida a jihar Edo tun bayan ƙirƙiro ta a shekarar 1991.

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa sabon SSG, ya ba ɗan tsohon shugaban APC babban muƙami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane alƙawari sabon gwamnan Edo ya yi?

A jawabin da ya yi wajen taron, Gwamna Okpebholo ya yi alƙawarin cewa da shi da mataimakinsa ba za su ci amanar da mutanen jihar suka ɗamka a hannunsu ba.

Ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen jindaɗin al'umma da inganta rayuwarsu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da rahoton.

"A yau, a hukumance kun ba ni haƙƙin jan ragamar jiharmu a matsayin gwamna na tsawon shekara huɗu masu zuwa."
"Ba za mu ci amanar wannan nauyin da kuka ba mu ba, da ni da mataimakin gwamna, Dennis Idahosa."
"Bunƙasa jin daɗin al'ummarmu shi ne babban fifiko a gare mu. Domin cimma hakan, za mu aiwatar da shirye-shirye, waɗanda za su bunƙasa tattalin arziƙi da rayuwar mutanenmu.

- Gwamna Monday Ighodalo

Gwamna Okpebholo ya yi naɗi a gwamnatinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Edo da aka zaba, Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin babban sakataren yada labarai kafin rantsuwarsa a ranar 12 ga Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan tashin bam a babban birnin jihar Arewa

Fred Itua, babban dan jarida ne wanda aka shaide shi da kwarewa a aikinsa, kuma ya taba aiki a matsayin mataimakin editan siyasa a jaridar The Sun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng