Matasa Sun Kashe Masu Karɓar Haraji a Kasuwa, an Shiga Fargaba
- Rahotanni da suka fito daga jihar Delta na nuni da cewa wasu masu karban haraji sun hadu da ajalinsu a cikin wata kasuwa
- Lamarin ya faru ne biyo bayan takun saƙa da ake samu tsakanin kabilu guda biyu a kan wanda yake da ikon karɓar haraji a cikinsu
- Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an samu yamutsi a kasuwar kafin daga baya a bude wuta kan masu karbar harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - An samu yamutsi a babbar kasuwar Ughelli a jihar Delta yayin da ake tsaka da karban haraji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe mutane biyu daga cikin masu karban harajin yayin da rikicin ya yi ƙamari.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin karban haraji a jihar Delta
Bincike ya tabbatar da cewa ana samun takun saƙa a tsakanin mutanen Ekiuyobe da Iwhereko a karamar hukumar Ughelli ta Arewa.
An tabbatar da cewa rikicin ya samo asali ne a kan wanda zai rika karban haraji a kasuwar Ughelli a tsakanin yankunan.
Yadda aka kashe masu karɓar haraji
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa ana tsaka da karɓan haraji da cin kasuwa ne aka fara jin karar harbe harbe.
Nan take wasu matasa suka bude wuta ga wani matashi mai suna Onome da aka fi sani da Oyibo a cikin kasuwar kuma ya fadi ya mutu.
Bayan haka, matasan sun harbi wani mai karbar haraji mai suna Nathaniel wanda aka tafi da shi asibiti, sai ya mutu a can.
Bayanin hukumomi a jihar Delta
Shugaban karamar hukumar Ughelli ta Arewa, Olorogun Jaro ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tura jami'ai domin ɗaukar matakin gaggawa.
Daily Post ta wallafa cewa Olorogun Jaro ya kara da cewa a zuwa gaba kadan za su samu cikakken rahoto kan hakikanin abin da ya faru kuma za su yi bayani ga jama'a.
Sai dai wani dattijo da ya so a ɓoye sunansa ya ce kisan yana da alaka da matsafa ne ba karɓan haraji ba.
An kama yan fashi a jihar Edo
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a Edo ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi sun yi fashi da makami a gidan wani mutum.
Bayanan yan sanda sun tabbatar da cewa an yi fashi da makamin ne a Ibie ta Kudu a karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng