Yan Ƙungiyar Lakurawa Sun Karbe Matsayin Sarakuna, Sun Kafa Sharaɗi a Arewa
- Ƴan ta'addan kungiyar Lakurawa sun karɓe ayyukan sarakunan gargajiya a kauyukan Kebbi da ke Arewa maso Yamma
- Bulama Bukarti ya ce a yanzun duk tafiyar kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma a jihar Kebbi sai ka haɗu da Lakurawa
- Lauya kuma ɗan fafutukar kare hakkin ɗan adam ya ce kungiyar ta kai shekara shida a Najeriya kuma za ta iya zama mai haɗari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi - Audu Bulama Bukarti ya ce mayaƙan sabuwar kungiyar ta’addanci, Lakurawa, sun karbe ayyukan sarakuna a wasu garuruwa a jihar Kebbi.
Bulama, ɗan gwagwarmayar kare haƙkin ɗan adam ya ce ƴan ta'adda suna shiga tsakanin mutane kamar dai yadda aka san sarakuna na yi.
Lauyan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na siyasa a yau na ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kungiyar ta kasance a Najeriya tsawon shekaru shida da suka gabata, yana mai cewa "tana iya zama ƙungiya mai hadari nan gaba."
Ƴan lakurawa za su iya zama haɗari
A ruwayar Daily Trust, Bulama ya ce:
"Idan ba ku manta ba, Boko Haram sai da ta zama ƙungiyar ta'addanci ta duniya amma ba abin da aka yi sai da ta yi shekaru tana ayyukanta, ta tara makamai, kudi ta hanyar garkuwa da mutane."
"Wannan ƙungiyar dai ba ta kai matakin Boko Haram ba ta fuskar sanin zamani, kashe-kashe da gogewa amma duk da haka tana iya zama mai haɗari. Ba za ka yi tafiyar kilomita biyar a Kebbi ba a haɗu da Lakurawa ba.
Ƙauyukan da ke kewaye da hedikwatar kananan hukumomin Kebbi suna karkashin ikon Lakurawa. Yanzu haka sun zama alƙalai, idan ka na da matsala ko saɓani da maƙwabci su ake kai wa ƙara, sun hana sarakuna komai."
- Bulama Bukarti.
Ƴan Lakurawa sun karɓe matsayin sarakuna
Bulama ya ƙara da cewa sarakuna ba su da wani zaɓi face su yi masu biyayya domin duk wanda ya ɗaga masu yatsa za su kashe shi ne kawai.
A cewarsa, idan makiyaya suka yi wa manoma ɓarna a gonaki, ƴan Lakurawa ke shiga tsakani kuma su sa a biya diyya ga wanda ake yi ɓarna.
Sojoji sun samu galaba a Zamfara, Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kebbi da Zamfara.
Jami'an tsaron sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa ciki har da na ƙungiyar Lakurawa da ta bayyana a cikin ƴan kwanakin nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng