Ta Faru Ta Kare, Gwamnati Ta Sanya Ranar Cefanar da Kadarorin Babban Banki
- Hukumar inshorar bankuna (NDIC) za ta fara siyar da kadarorin bankin Heritage ranar 4 ga Disamba, 2024, a kasa baki daya
- Daraktan sadarwa na NDIC, Bashir Nuhu, ya ce kamfanoni da daidaikun mutane na iya duba kadarorin kafin ranar gwanjonsu
- NDIC ta sanar da za a cefanar da kadarorin bankin ne a Abuja, Legas da sauran wurare tare da yin karin bayani ga jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar Inshorar Bankuna ta Najeriya (NDIC) ta sanar da fara sayar da kadarorin bankin Heritage daga ranar 4 ga watan Disamba, 2024.
Daraktan sadarwa na NDIC, Bashir Nuhu, ya ce cefanar da kadarorin ya yi daidai da ikon hukumar na gudanar da rufewar bankunan da suka ruguje.
Masu sha'awar sayen kadarorin bankin za su iya gabatar da tayi a ofisoshin NDIC da ke Abuja, Legas, Bauchi, Kano, Enugu, da Fatakwal inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NDIC za ta sayar da kadarorin Heritage
Hukumar NDIC ta bayyana cewa, za ta yi adalci yayin gwanjon kadarorin bankin ta yadda wadanda suka cancanta za su samu damar saya.
Sanarwar Bashir Nuhu ta ce za a fi bai wa cibiyoyin kudi fifiko a yayin gwanjon kadarorin da nufin ci gaba da amfani da kadarorin da aka riga aka rufe.
Bashir Nuhu ya bayyana cewa kamfanoni da masu zaman kansu na iya nuna sha'awar sayen kadarorin, wanda zai tabbatar da tsarin ba kowa damar saye.
Ana iya duba kadarorin kafin ranar da za a yi gwanjonsu, domin tantance kimar su sosai. Haka kuma za a samu bayanai a shafukan NDIC da jaridu.
CBN ya soke lasisin bankin Heritage
A baya bayan nan ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankin Heritage bisa ga rashin kudaden tafiyar da bankin.
Bayan haka, NDIC ta fara tantancewa da biyan hakkokin masu asusu a bankin Heritage kudaden da suka yi ajiya.
Jerin kadarorin da za a sayar ya hada da gidaje 48, motoci, da kayan aiki a wurare 62.
Dalilin CBN na soke lasisin Heritage
Tun da fari, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN ya kwace lasisin bankin Heritage Plc saboda ya karya sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020.
CBN ya ce hukumar gudanarwar Heritage da ma kwamitin amintattu sun gaza inganta ayyukan hada-hadar kudin bankin, wanda ya ke barazana ga daidaiton kudin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng