'Cututtuka na Shigowa Najeriya saboda Yunwa,' NLC Ta Tono Bayanai

'Cututtuka na Shigowa Najeriya saboda Yunwa,' NLC Ta Tono Bayanai

  • Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatoci a matakai daban daban da su fitar da shirye shirye domin tallafawa talakawan Najeriya
  • Shugaban kwadago ya bayyana cewa a yanzu haka yan Najeriya na fama da matsananciyar yunwa da ya kamata a tausayawa musu
  • Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnati ne yayin wani taro na musamman da yan kwadago suka yi a birnin Fatakwal a makon da ya wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kungiyar kwadago ta yi kira na musamman ga shugabanni kan saukakawa al'ummar Najeriya.

Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya koka a kan yadda farashin man fetur yake kara hauhawa kullum a Najeriya.

Yan kwadago
Yan kwadago sun bukaci magance yunwa a Najeriya. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce yanzu cututtuka sun fara bayyana a Najeriya saboda masifar yunwa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta bukaci kawo saukin rayuwa

Shugaban NLC na kasa, Jeo Ajaero ya ce akwai takaici kan yadda gwamnatoci ke jan ragamar tattalin Najeriya.

Punch ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce lamarin ya kara jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali ta inda ba su iya samun wadataccen abinci.

Cutar kwashoko ta dawo inji NLC

Kungiyar kwadago ta ce an fara samun cututtuka kamar kwashoko suna kara ɓullowa Najeriya saboda matsalar yunwa.

NLC ta ce a yanzu haka ma'aikata na kokuwa tsakanin sayen magani da kayan abinci idan ba su da lafiya.

A karkashin haka, Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnati kan samar da tsare tsaren da za su saukaka rayuwar al'ummar Najeriya.

NLC ta koka a kan karin kudin fetur

Kwamared Joe Ajaero ya ce akwai damuwa a kan yadda ake samun karin kudin litar man fetur a Najeriya a kai a kai.

A cewar Joe Ajaero, karin kudin man fetur na sanya tashin farashin kayayyaki ta inda ma'aikata suke gagara yin sayayya.

Kara karanta wannan

An sake gabatar da bukatar maido tallafin man fetur ga Tinubu

DSS ta shiga rikicin yan kwadago

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta fara kokarin sasanta rikicin da ya shiga tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin rarraba wuta.

NLC na zargin kamfanin rarraba hasken lantarki da ke Ikeja da take hakkin ma'aikatansa duk da an zauna tare da cimma matsaya a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng