Jami'an DSS Sun Shiga Tsakanin NLC da Kamfanin Wutar Lantarki

Jami'an DSS Sun Shiga Tsakanin NLC da Kamfanin Wutar Lantarki

  • Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta fara kokarin sasanta rikicin da ya shiga tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin rarraba wuta
  • NLC na zargin kamfanin rabbaba hasken lantarki da ke Ikeja da take hakkin ma'aikatansa duk da an zauna tare da cimma matsaya a baya
  • Mataimakin sakataren kungiyar ma’aikatan kamfanonin lantarki, Kwamred Mbang Ntukubes ya ce kamfanin na Ikeja na cin zarafin ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shiga tsakani domin kawo karshen dambarwar da ke tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin wutar lantarki da ke Ikeja, Lagos.

Kungiyar kwadago ta NLC ta na zargin kamfanin rarraba wutar lantarkin na Ikeja da cutar da ma’aikatan da ta dauka aiki.

Kara karanta wannan

"Za a Cigaba da Samun Matsalar Lantarki:" TCN Ya Fadi Lokacin Magance Rashin Wuta

Jami'a DSS
NLC da kamfanin wutar lantarki a Legas sun samu sabani Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A labarin da ya kebanta da Daily Trust, mataimakin sakataren kungiyar ma’aikatan kamfanonin lantarki, Kwamred Mbang Ntukubes ya fadi zargin da su ke yi wa kamfanin da ke Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rikicin NLC da kamfanin wutar lantarki

Kwamred Mbang Ntukubes ya bayyana takaicin yadda kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Ikeja ya ki mutunta yarjejeniyarsu.

Ya zargi kamfanin da mayar da ma’aikatansa bayi duk da zama da aka rika yi tare da cimma manufar kyautata rayuwar ma’aikata.

NLC ta fadi matsalarta da kamfanin wutar lantarki

Mataimakin sakataren kungiyar ma’aikatan kamfanonin rarraba wutar lantarki, Kwamred Mbang Ntukubes ya zargi kamfanin rarraba wuta na Ikeja da korar ma’aikata bakatatan.

Ya bayyana hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyace su domin yadda za a samu matsaya tare da kawo karshen dambarwar.

Kungiyar NLC ta fusata da batun albashi

A wani labarin kun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta sanar da ranar da za ta tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan saboda yadda wadansu jihohin kasar nan ke kin biyan mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Likitoci sun gana da gwamnan Kano, sun canza matsaya kan shiga yajin aiki

Uwar kungiyar ta kasa ta zargi gwamnoni da har yanzu ba su kai ga fara biyan mafi karancin albashin ba da kin mutunta doka, tare da umartar 'ya'yan kungiyar su shirya fara zanga zanga a Disamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel