Tinubu zai Gabatar da Bukatu 2 a Taron Kasashen Musulunci da Larabawa a Saudiyya
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai mika wasu manyan bukatu a taron kasashen Larabawa da Musulmi a Saudiyya
- Daga cikin bukatun da ake sa ran Bola Tinubu zai gabatar akwai dakatar da yakin da Isra'ila ke kai wa kan Falasdinawa
- Tinubu ya sauka a birnin Riyadh da ke Saudiyya domin halartar babban taron da za a gudanar da tsawon kwanaki biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Saudi Arabia – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Riyadh da ke Saudiyya domin halartar taron Larabawa da kasashen Musulunci inda zai mika bukatu kan yakin Isra'ila.
An gano wasu daga cikin bukatun da shugaba Tinubu zai gabatar a gaban taron bayan an fara za su danganci yakin da aka shafe sama da shekara ana yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Yarima Mohammed AbdulRahman ne ya tarbi Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadi a filin jirgin Sarki AbdulAziz.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukatun da Tinubu zai gabatar a Saudiyya
Voice of Nigeria ta tattaro cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai bukaci tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke kai wa kan Falasdinawa.
Haka kuma ana sa ran shugaban zai nemi a samar da tsarin kasa biyu a Falasdinu yayin da Isra'ila ke kokarin fitar da mazauna Gaza da wasu sassan daga muhallansu.
Abin da za a tattauna a kasar Saudiyya
Taron kasashen Larabawa da na musulunci da ke gudana a Saudiyya ya na mayar da hankali a kan yakin da Isra’ila ta kaddamar a kan Falasdinawa.
Dakarun Isra’ila na IDF sun kashe Falasdinawa akalla 43,391 tun bayan fara yakin a shekarar 2023 zuwa yanzu, daga cikinsu akwai kananan yara da mata.
Shugaba Tinubu ya sauka a Saudiyya
A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a filin jirgin Yarima Mohammed AbdulRahman da ke Saudiyya domin halartar kasashen Larabawa da na Musulunci.
Za a gudanar da taron na kwanaki biyu inda ake hasashen za a tattauna manyan batutuwa da su ka hada da kasuwanci, yaki da ta'addanci da ci gaban ababen more rayuwa tsakanin kasashen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng