Gwamna a Arewa Zai Fara Riƙe Albashin Wasu Ma'aikata daga Watan Nuwamba

Gwamna a Arewa Zai Fara Riƙe Albashin Wasu Ma'aikata daga Watan Nuwamba

  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya ce ba za a biya ma'aikata albashin watan Nuwamba ba matuƙar ba su mallaki lambar KWSRRA ba
  • Kwamishinar kudi, Dr. Hauwa Nuru ce ta bayyana hakan a wata sanarwa, ta ce an jima da ba ma'aikata umarnin su garzaya su yi rijista
  • Ta ce daga watan Nuwamba, gwamnatin Kwara za ta dakatar da albashi da alawus na ma'aikatar da ba su yi rijista a hukumar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Gwamnatin Kwara karkashin jagorancin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ta ɗauki mataki mai tsauri kan mallakar lambar zama cikakken ɗan jiha.

Gwamnatin ta bayyana cewa duk ma'aikacin da bai mallaki lambar zama ɗan jiha ta hukumar KWSRRA ba, ba zai ga albashin watan Nuwamba, 2024 ba.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
Gwamnatin Kwara ta ce ba za ta biya ma'aikatan da ba su da rijistar KWSRRA albashi a watan Nuwamba ba Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Twitter

Gwamna ya tilasta mallakar lambar KWSRRA

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana bayan sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga ta kashe mutum 15

Sakataren yaɗa labaran ma'aikatar kudi ta Kwara, Babatunde Abdulrasheed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yau Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce doka ta ba hukumar KWSRRA damar tattara bayanan da suka dace na kowane mazaunin jihar Kwara.

Haka nan kuma doka ta ba hukumar damar bai wa kowane ɗan jihar lambar shaidar zama ta yadda gwamnati za ta samu bayanai domin yiwa jama'a aiki.

Gwamnatin Kwara za ta fara riƙe albashin ma'aikata

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun kwamishinar kudi, Dr. Hauwa Nuru ta ce:

"A kwanakin baya gwamnati ta umarci dukkan ma’aikatan jihar da suka hada da na kananan hukumomi 16 da su tabbata sun kammala rajista a KWSRRA.
"Daga Nuwamba 2024, dukkan ma'aikatan da ba su yi rajista da wannan hukuma ba, ba za a biya su albashi ko alawus-alawus dinsu ba.
"Wannan rijista dai tana da matuƙar muhimmanci wajen haɗa bayanai domin yi wa jama'ar jihar Kwara aiki daidai gwargwado."

Kara karanta wannan

Bayan ayyana ilimi kyauta, gwamna a Arewa ya kawo sabon tsari a manyan makarantu

Sanarwar ta ruwaito Dakta Hauwa Nuru na cewa tsarin yin rijistar zai taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa arzikin Kwara da tsare-tsare masu inganci, Daily Trust ta kawo.

Gwamnatin Kwara ta ƙarawa ma'aikata alawus

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Kwara ta sanar da shirinta na ba ma'aikatan jihar da ma na kananan hukumomi alawus na watanni uku.

Kwamishiniyar kudi ta jihar, Hauwa Nuru ta bayyana cewa ma'aikata za su samu tallafin kudin daga Oktoba zuwa Disamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262