Abuja Ta Fada cikin Duhu, 'Yan Ta'adda Sun Lalata Turken Wayoyin Wutar Lantarki
- Kamfanin wutar lantarki na Najeriya ya bayyana cewa 'yan ta'adda sun kai hari kan turken wayoyin wutar Lokoja-Gwagwalada
- TCN ya bayyana cewa injiniyoyi sun gano an sace igiyoyin aluminium guda biyu, wanda ya kawo cikas ga samun wuta a Abuja
- Kamfanin ya nemi taimakon al’umma domin dakile ayyukan 'yan ta'adda da ke haddasa matsaloli a tushen wutar kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da wani hari da aka kai a turken layin wutar lantarki mai karfin 330kV na Lokoja-Gwagwalada.
Kamfanin TCN ya ce harin da 'yan ta'addan suka kai kan turakun wutar wanda ya shafi husumiyoyi guda uku.
'Yan ta'adda sun lalata wutar lantarki
Harin, wanda ya faru a ranar 9 ga Nuwamba, ya kawo cikas ga isar da wutar lantarki a yankin Abuja da kewaye, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Injiniyoyin TCN sun yi kokarin gyara matsalar amma hakan ya ci tura. An ce sun gano cewa an sace wasu daga cikin igiyoyin aluminium guda biyu.
Wannan lamari na cikin jerin hare haren da 'yan ta'adda ke kai wa turken wayoyin wutar lantarki wanda ke ke haddasa matsala ga wutar lantarki na Najeriya.
Sassan Abuja sun shiga cikin duhu
Lalata wutar yana shafar babban tushen wutar lantarki na kasar, kuma TCN ta kira yi ga al'umma da su taimaka wajen dakile wannan ta'asa.
A halin yanzu, ana kokarin samo kayan da za ayi amfani da wasu wajen maye gurbin igiyoyin da aka sace, a cewar rahoton Punch.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu sassan Abuja suna cikin duhu tun bayan da 'yan ta'addan suka lalata turken wutar, lamarin da ke zuwa bayan jerin durkushewar tashar wuta.
An lalata hasumiyar TCN karo na uku
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan ta'adda sun lalata layin wutar Damaturu-Maiduguri wanda ke samar da wutar lantarki ga garuruwan Damaturu.
Rahoto ya nuna cewa wannan ne karo na uku a cikin yan watanni da yan ta'adda ke lalata hasumiyar TCN da ke kai wuta yankin a cikin yan watanni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng