Zababben Gwamnan APC Ya Yi Nadin Farko Tun Kafin a Rantsar da Shi, An Samu Bayanai

Zababben Gwamnan APC Ya Yi Nadin Farko Tun Kafin a Rantsar da Shi, An Samu Bayanai

  • Zababben gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin babban sakataren yada labaransa
  • Fred Itua, wanda ke da kwarewa mai yawa a aikin jarida, zai taimaka wajen inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma
  • Wannan nadin da Okpebholo ya yi shi ne aikin farko da gwamnatinsa ta yi tun kafin a rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Gwamnan Edo da aka zaba, Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin babban sakataren yada labarai kafin rantsuwarsa a ranar 12 ga Nuwamba, 2024.

Wannan nadin shi ne aikin farko na gwamnatin Okpebholo mai zuwa.

Zababben gwamnan jihar Edo ya yi nadin farko kafin shiga ofis.
Zababben gwamnan Edo ya nada sakataren watsa labarai, nadin farko kafin shiga ofis. Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Zababben gwamna ya yi nadin farko

Fred Itua, babban dan jarida ne wanda aka shaide shi da kwarewa a aikinsa, kuma ya taba aiki a matsayin mataimakin editan siyasa a jaridar The Sun.

Kara karanta wannan

'Ka hana Wike, gwamnoni ba alkalai motoci da gidaje,' SERAP ta fadawa Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwarewarsa a fannin jarida za ta taka rawa sosai wajen tabbatar da nagartacciyar sadarwa a sabuwar gwamnatin Monday Okpebholo.

Zababben gwamnan ya jaddada muhimmancin sadarwa a gwamnatinsa, wanda nadin da ya yi wa Fred Itua ya kara tabbatar da hakan, a cewar rahoton Channels TV.

Manufar nada sakataren watsa labarai

An ce nadin Fred Itua yana nuna aniyar Okpebholo na inganta dangantaka tsakanin gwamnati da al’umman Edo ta fuskar isar da sako a kan lokaci.

Sabon babban sakataren yada labaran zai taka rawa wajen isar da sakonnin gwamnati ga al'ummar jihar musamman na ayyukan da za ta aiwatar.

Ana kuma ganin cewa nadin da Gwamna Okpebholo ya yi wa Fred Itua ya dace da hangen nesan sa na kafa gwamnati mai gaskiya da kuma mutunta fannin sadarwa.

Trump ya yi nadin farko kafin rantsuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi nadin farko a gwamnatinsa kafin rantsuwar kama aiki.

Kara karanta wannan

'An rasa inda yake': An zargi Gwamna da tserewa daga gidan gwamnati tun Juma'a

An ce Trump ya nada Susie Wiles a matsayin shugabar ma'aikatan fadarsa ta White House, ita ce mace ta farko da ta rike mukamin a tarihin Amurka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.