Arewa: Ana Shirin Kawar da Yunwa, Gwamna Ya Kawo Noman Zamani
- Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da noma da kayan aiki na zamani a damunar bana inda ake fatan samun kayan abinci mai tarin yawa
- Gwamna Umaru Muhammad Bago ya fara shirin noman ne a kokarinsa na samar da abinci da zai wadata yan Najeriya sosai
- Umaru Muhammad Bago ya bayyana cewa amfani da kayan aikin noma na zamani zai taimaka wajen rage hasara da ake yi sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta fara girbin kayan abinci a karkashin shirin noma da ya gudanar a damunar bana.
Gwamna Umaru Muhammad Bago da kansa ya kaddamar da girbin kayan abinci a cikin wata gona.
Legit ta tatttaro bayanai kan yadda nomar ta gudana ne a cikin wani sako da gwamna Umaru Bago ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka fara nomar zamani a Neja
Gwamna Umaru Muhammad Bago a fara shirin noma da injinan zamani domin samar da wadataccen abinci.
Umaru Bago ya bayyana cewa a bana kawai jihar ta noma hekta sama da 100,000 a sassa daban daban na Neja.
Gwamnan ya ce an tura motocin zamani da za su rika girbin kayan abinci sama da 100 a gonakin da suka noma kuma motocin za su rage hasara da ake samu da kashi 80% zuwa 90%.
Me gwamnati ta noma a jihar Neja?
Gwamna Umaru Muhammad Bago ya bayyana cewa sun noma masara, waken suya, shinkafa, dawa, riɗi da gero.
Idan aka kammala tatttaro amfanin gona, gwamnatin za ta samu kayan abinci na miliyoyin ton da za a amfana da su wajen yaki da yunwa a Najeriya baki daya.
Aikin kwamitin lura da farashi a Neja
Gwamna Bago ya umarci yan kwamitin lura da farashin kayan abinci da su fara aiki wajen ganin farashi bai tashi ba.
Umaru Bago ya bukaci yan kwamitin da su rika saka ido a kan masu kudi da suke sayen kayan abinci suna boyewa domin farashi ya karu.
Tinubu ya yi magana kan noma
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya kan yadda za a shawo kan tsadar kayan abinci.
Ta bakin hadiminsa, ya ce akwai bukatar kowa ya natsu ya ba da gudunmawa wajen gina kasa, musamman duba da yanayin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng