Gwamna Ya Kai Dauki ga Iyalan Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Kashe a Jiharsa
- Gwamnan jihar Kebbi, ya yi ta'aziyyar mutanen da ƴan bindiga suka kashe a yankin Mera na ƙaramar hukumar Augie
- Dakta Nasir Idris ya ba da gudunmawar Naira miliyan 50 ga iyalan mutane 15 da ƴan bindigan suka kashe a harin ta'addancin sa suka kai
- Gwamnan ya kuma buƙaci jama'a da su riƙa ba da sahihan bayanai waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen masu aikata laifuka a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi alhini kan harin da ƴan bindiga suka kai wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum 15.
Gwamna Nasir Idris ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 don tallafawa iyalan mutane 15 ɗin da harin na bindiga ya rutsa da su a yankin Mera na ƙaramar hukumar Augie.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa Ahmed Idris ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya koka kan harin ƴan bindiga
Gwamnan ya bayyana harin a matsayin wani lamari mai ban takaici na rashin tausayi.
Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe mutane 15 tare da yin awon gaba da shanu sama da 100 a Mera da ke ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi.
"A madadin gwamnatin jihar Kebbi, muna miƙa sakon ta’aziyyarmu ga Sarkin Argungu, mai martaba Alhaji Sama’ila Muhammadu-Mera, da al’ummar Mera."
- Ahmed Idris
Gwamna Nasir ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da hukumomin tsaro domin yakar miyagun laifuka a faɗin jihar Kebbi.
Gwamnan ya kuma buƙaci jama’a da su goyi bayan wannan ƙoƙarin ta hanyar bayar da sahihin bayanai.
Sojoji sun tabbatar da ɓullar ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da bullar sabuwar kungiyar yan ta’adda a jihohi biyu da ke Arewacin kasar nan.
Tabbacin rundunar ya zo bayan rahotanni sun bayyana ɓullar ƙungiyar yan ta’adda mai tsatstsauran ra’ayi da ake kira da lakurawa a Sakkwato.
Asali: Legit.ng