Garambawul: Tsohon Dan Majalisa Ya ba Tinubu Shawarar Ministocin da Za a Kora

Garambawul: Tsohon Dan Majalisa Ya ba Tinubu Shawarar Ministocin da Za a Kora

  • Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya ba shugaban ƙasa, Bola Tinubu shawara kan ministocinsa
  • Dakta Wunmi Bewaji ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya sake korar wasu ministoci a gwamnatinsa da ba su taɓuka komai
  • Ya yi nuni da cewa yana fatan garambawul ɗin da Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa ba shi ne na ƙarshe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Dakta Wunmi Bewaji, ya nemi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ƙara korar wasu ministocin da ba su taɓuka komai.

A kwanakin baya ne Shugaba Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul inda ya kori ministoci shida tare da naɗa wasu sababbi guda bakwai.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

Am bukaci Tinubu ya kori ministoci
Dan majalisa ya bukaci Bola Tinubu ya kori ministoci Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Wace shawara ɗan majalisar ya ba Tinubu?

A wata hira da ya yi da jaridar Tribune, Bewaji, ya bayyana cewa tuntuni ya kamata a ce Tinubu ya yi wa majalisar ministocin garambawul.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ɗan majalisar ya ƙara da cewa har yanzu akwai sauran ministocin da ba su taɓuka komai a gwamnatin da Tinubu ke jagoranta.

"Tuntuni ya kamata a ce an yi garambawul ɗin, wannan wanda muka gani an yi yanzu, ina so na yarda cewa shi ne na farko, ba gamawa aka yi ba."
"Saboda har yanzu akwai baragurbi a cikin gwamnatin waɗanda ya kamata a ce an kore su daga aiki."

- Dakta Wunmi Bewaji

"An ɓarnata kuɗin Najeriya", Bewaji

Jaridar Daily Trust wacce ta bibiyi hirar ta ce da aka tambaye shi ya yi magana kan manufofin gwamnatin Tinubu da kuma tasirinsu ga ƙasar nan, sai ya ka da baki ya ce:

Kara karanta wannan

"Za a zage ku," Abin da Tinubu ya faɗawa sababbin Ministoci bayan rantsar da su

"Gwamnatin da ta hau mulki kimanin shekara ɗaya da rabi da suka wuce, na yi imanin cewa ba za a ga amfanin manufofinta da sauri ba, saboda mun yi wasa da kuɗaɗen Najeriya."
"A lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ta yi almubazzaranci da ɗimbin dukiya."
"A zamanin Goodluck Jonathan muna sayar da man fetur a dala 140 kan kowace ganga kuma Najeriya tana haƙo ganga miliyan 2.5 a kowace rana, amma mun ɓarnatar da komai."
"Mun ƙarar da asusun rarar man fetur, mun ƙarar da asusun ajiya na kuɗaɗen waje. Sannan Buhari ya zo. Idan da Buhari ya ƙaddamar da waɗannan sauye-sauyen, a cikin shekara takwas da ya yi, watakila da ba mu shiga halin da muka tsinci kanmu a ciki ba yanzu."

Ƙungiya ta ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin muƙamin minista.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci Tinubu da ya naɗa wasu gogaggun mutane a matsayin ministoci a shirin da yake yi na yiwa majalisar ministocinsa garambawul.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng