Remi Tinubu Ta Fadi Abin da Ta Sani kan Taron Addu'a saboda Tsadar Rayuwa

Remi Tinubu Ta Fadi Abin da Ta Sani kan Taron Addu'a saboda Tsadar Rayuwa

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi magana kan shirin gudanar da taron addu'o'i na ƙasa kan halin tsadar rayuwa
  • Remi Tinubu ta bayyana cewa ko kaɗan babu hannunta a jagorantar shirin inda ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya
  • Ta buƙaci jama'a da su riƙa tabbatar da bayanai kan ayyukanta ko ofishinta ta hanyoyin da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta musanta hannu a wani shirin taron addu’o’in da ake yi kan wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan.

Wasu rahotanni sun ce Remi Tinubu da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, za su jagoranci taron na kwanaki bakwai kan halin da ake ciki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula ƙasar waje, zai halarci muhimmin taro da ya shafi Musulunci

Remi Tinubu
Remi Tinubu ta ce babu hannunta a shirin taron addu'o'i kan tsadar rayuwa Hoto: Senator Oluremi Tinubu
Asali: UGC

Sai dai mai magana da yawun uwargidan shugaban ƙasar, Busola Kukoyi, ta musanta hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Busola Kukoyi ta bayyana cewa ko kaɗan babu hannun uwargidan shugaban ƙasan a shirin gudanar da addu'o'in.

Me Remi Tinubu ta ce kan taron addu'o'i

Ta bayyana rahotannin a matsayin na ƙanzon kurege sannan ta buƙaci jama'a da su yi watsi da su.

"Ana sanar da jama’a cewa uwargidan shugaban ƙasan Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ba ta shirya taron addu'a na ƙasa ba."
"Labaran da ke yawo a kafofin watsa labarun ba su da tushe ballantana makama. Don haka, duk wanda ya ci karo da labarin taron addu'o'i na ƙasa, to ya yi watsi da shi a matsayin ƙarya."
"Ana shawartar jama’a da su riƙa tabbatar da sahihancin duk wani labari ko wani abu da ya shafi uwargidan shugaban ƙasa ko ofishinta ta hanyoyin da suka dace."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan majalisa sun mika bukata wajen gwamnati kan yaran da aka tsare

- Bisola Kukoyi

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Atiku martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki zafi bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakan da ta ɗauka kan tattalin arziƙi.

Fadar shugaban ƙasan ta ce babu dalilin da Atiku Abubakar zai rika kwatanta matakan gwamnati da ƙudurorinsa waɗanda ba a taɓa gwadasu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng