Shugaba Tinubu Zai Lula Ƙasar Waje, Zai Halarci Muhimmin Taro da Ya Shafi Musulunci
- Fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu zai kama hanyar zuwa Saudiyya gobe Lahadi domin halartar taron ƙasashen Larabawa da Musulunci
- Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu tare da jaddada bukatar tsagaita wuta
- Ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024 za a fara taron kuma za a tattauna kan rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai lula zuwa ƙasar Saudiyya a gobe Lahadi domin halartar taron haɗin kan ƙasashen Larabawa da Musulunci.
Za a fara taron ne idan Allah ya kaimu ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024 kuma ana sa ran shugabannin za su tattauna kan rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakkiya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa shafin X yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya ce taron ya saba gudana bisa gayyatar Sarki Salman da yariman Saudiαyya mai jiran gaso, Mohammed bin Salman.
Abin da Bola Tinubu zai magana akai a taron
Hadimin shugaɓan ƙasar ya ce Bola Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu wanda har yanzu ƴa ki ci kuma ya ƙi cinyewa.
"A taron Shugaba Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu, inda zai jaddada matsayar Najeriya na tsagaita wuta cikin gaggawa da warware matsalar cikin lumana.
"Najeriya za ta kuma ba da shawarar sake yin kokarin farfado da tsarin kasashe biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin."
- Bayo Onanuga.
Manyan jiga-jigan da za su raka Tinubu
Manyan ƙusoshin gwamnati da za su raka Bola Tinubu sun haɗa da ministan harkokin ƙasashen ketare, Ambadada Yusuf Tuggar da ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris.
Sauran sune mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da daraktan hukumar tattara bayanan sirri NIA, Mohammed Mohammed.
Fadar shugaban ƙasa ta ce bayan kammala taron, Bola Tinubu zai dawo Abuja.
Bola Tinubu ya taya Trump murna
A wani rahoton, mun kawo maku cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya zababben shugaban Amurka, Donald Trump murnar samun nasara a zaɓe.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bukaci ƙara karfafa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Amurka.
Asali: Legit.ng