TCN: Ƴan Najeriya Za Su Ɗauki Lokaci Ba Wutar Lantarki, An Gano Matsaloli 3 a Arewa

TCN: Ƴan Najeriya Za Su Ɗauki Lokaci Ba Wutar Lantarki, An Gano Matsaloli 3 a Arewa

  • Kamfanin raba wuta TCN ya gano asalin layukan wutar lantarki uku da ke yawan ba da matsala a Najeriya
  • An ruwaito cewa tuni aka fara aikin gyara domin kawo karshen yawan ɗaukewar wuta kuma ana tsammanin gyaran zai ɗauki akalla makonni uku
  • Legit Hausa ta tattaro cewa an kawo wuta a wasu sassan ƙasar nan bayan lalacewar da ta yi ranar Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Aikin gyaran manyan layukan wutar lantarkin da ake yi domin kaucewa yawan lalacewa zai ɗauki aƙalla makonni uku kafin a gama.

Wannan na zuwa ne bayan lalacewar da layin wuta na ƙasa ya ƙara yi ranar Alhamis da ta gabata, lamarin da ya jefa ƴan Najeriya a duhu.

Kara karanta wannan

"Wata 3 kenan muna cikin duhu" Gwamna ya koka kan rashin wutar lantarki a jiharsa

Layin wutar lantarki.
Gyaran layukan wutar lantarki zai ɗauki makonni 3 a Najeriya Hoto: TCN
Asali: UGC

The Nation ta tattaro cewa wutar lantarki a Najeriya ta samu matsala sau biyu a makon da ya shige, na farko ranar Talata, na biyu kuma ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TCN ya gano tushen matsalar wuta

Kamfanin rarraba wuta na ƙasa watau TCN ya ce ya gano wurare uku da suka fi kawo matsala da lalacewar wutar lantarki.

Layukan da aka gano suna yawan bada matsala sun haɗa da layin wuta da ke Shiroro a jihar Neja da kuma na Jebba da Ganmo duk a jihar Kwara.

Daraktan sashin harkokin rarraba wuta na TCN, Injiniya Gbenga Ajiboye ya ce tuni aka samar da isassun kayayyakin da za a yi wannan gyara.

Gyaran wuta ya kankama

A wata hira ta wayar tarho, Ajiboye ya ce an kwashe kayan gyaran daga tashohin wuta zuwa wurararen guda uku.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi maganar batun sake lalacewar tashar lantarki a yau

Kamfanin TCN ya tabbatar da cewa zuwa karfe 4:00 na yamma, kamfanonin samar da wuta GenCos su samar da 1,844MW na wutar lantarki.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan Najeriya sun fara samun wuta a wasu sassan ƙasar nan bayan matsalar da ta afku a ranar Alhamis.

An fara dawo da wuta a Najeriya

Abdulhafiz Tukur, wani mazaunin garin Dabai a jihar Katsina ya tabbatarwa wakilin Legit Hausa cewa an kawo masu wuta da safiyar yau Asabar.

"Eh an kawo wuta da safen nan wajen karfe 8:00 kuma har zuwa yanzu da nake magana da kai akwai wutar."
"Muna kira ga gwamnati ta kawo karshen wanan matsalar ta yawan lalacewar wuta domin tana taɓa kasuwanci da wasu harkokin yau da kullum," in ji shi.

Wata uku babu wuta a Bayelsa

A wani rahoton an ji cewa Gwamna Douye Diri ya koka kan lalacewar wutar lantarki tsawon watanni uku a jihar Bayelsa saboda katsewar wasu na'u'rorin TCN.

Diri ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tare da kamfanin samar da wuta na ƙasa watau TCN domin gyara matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262