Mazauna Abuja Sun Gaji da Halin Wike, Sun Fito Zanga Zanga Neman Agajin Tinubu
- Mazauna babban birnin tarayya sun zargi Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike da rushe masu gidaje ba bisa ka'ida ba
- Lauyan mazauna babban titin Lugbe Airport sun zargi Ministan da jawo wa mutane akalla 1,000 matsalar muhalli
- Wannan na zuwa bayan an zargi ministan da rusa wadansu gidajen akalla 100 ba bisa ka'ida ba tare da jawo asarar N200bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mazauna birnin tarayya Abuja sun fito nuna fushinsu kan yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ke cigaba da rushe gidajen jama’a ba tare da la’akari da kokensu ba.
Masu zangar-zangar sun fito ne daga yankin Ruga da ke babban titin Lugbe-Airport a babban birnin tarayya Abuja, su ka nemi daukin shugaban kasa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mazauna garin Ruga sun bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta takawa Ministan Abuja, Nyesom Wike birki daga cigaba da rusau da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana rushe gidajen mazauna birnin Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin rusau da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kafa ya ruguje wasu gidaje a ranar Laraba, tare da rushe wasu gine-gine da ta ce an yi ba bisa ka’ida ba a garin Ruga.
Mazauna yankin sun bayyana cewa jami’an kwamitin sun dage masu kwanon da aka rufa gine-ginensu tare da kona wasu falankai.
Mazauna Abuja sun nemi daukin Tinubu
Lauyan mazauna Abuja da mahukuntan birnin ke rushewa muhallai, Deji Adeyanju ya bayyana cewa rusau da ake yi a halin yanzu zai shafi mutane akalla 15,000.
Deji Adeyanju ya ce su na kalubalantar rushen-rushen da ake yi, domin babu wasu kwararan dalilai da za su bayar da damar raba jama’a da muhallansu.
An zargi Wike da rushe gidajen Abuja
A baya mun wallafa cewa kungiyar masu gine gine a babban birnin tarayya Abuja ta zargi Ministan birnin, Nyesom Wike da rushe masu gidaje ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.
Kungiyar masu gine-gine ta HBAN ta zargi Minstan Abuja, Nyesom Wike da rushe gidaje sama da 100 a yankin Sabon Lugbe, wanda ake ce ya jawo asarar akalla Naira biliyan 200.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng