Gwamnatin Tarayya Ta Yi Maganar Batun Sake Lalacewar Tashar Lantarki a Yau
- Gwamnatin tarayya ta bayyana gaskiyar labari daga bangarenta game da lalacewar wutar lantarki a karo na 11 a 2024
- Masu kula da turakun wuta sun musanta labarin ranar Juma'a da ya ce tashar ta sake samun matsala ana tsaka da gyaranta
- Yan Najeriya sun fusata, kuma sun fara hakura da sha'anin lantarki kamar yadda wasu su ka shaidawa Legit a yammacin yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ƙaryata labarin cewa babbar tashar wutar lantarki a kasar nan ta sake lalacewa a karo na 11 a shekarar 2024.
A yau Juma'a ne aka rika yada labarin cewa wutar lantarkin Najeriya ta kuma lalacewa a daidai lokacin da ake kokarin gyaran wuta.
Wannan na kunshe a cikin wani sako da masu kula da turakun lantarkin kasar nan su ka wallafa a shafinsu na X mai suna Nigeria National Grid.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta karyata zancen lalacewar lantarki
Gwamnatin tarayya ta ce babu kamshin gaskiya a labarin cewa tashar lantarki a kasar nan ta sake lalacewa a ranar Juma'a, 8 Nuwamba, 2024.
Tuni jama'a su ka fara martani bisa ikirarin da gwamnati ta yi, ganin cewa an dauke wuta a wurare da dama.
Martanin jama'a kan lalacewar wutar lantarki
Mazauna Najeriya da ke amfani da shafukan sada zumunta, musamman shafin X sun yi rubdugu bisa ikirarin cewa karya ake a kan batun lalacewar wuta.
@theAmaizingJosh ya ce:
"Babbar tashar wutar lantarki ta fi aiki a X maimakon a zahiri."
@Iamkolotayo ya ce:
"Amma a hankali ake dauke wuta😳😳"
Wata mai sana'ar ruwan sanyi a Kano, Rafi'at ta bayyanawa Legit cewa dama sun fitar da rai a kan samuwar hasken lantarki a kasar nan.
Muhammad Bello Dabai kuma cewa ya yi:
"Allah Ya ba kowa kudin hada sola a bar masu wutarsu."
Lantarkin Najeriya ya sake lalacewa
A wani labarin mun ruwaito cewa babbar tashar lantarkin Najeriya ta sake samun matsala a karo na biyu a cikin kwanaki uku duk da wasu bangarorin dama babu wuta.
Lamarin bai yi wa yan kasa dadi ba wandanda su ka shafe akalla sama da wata guda ana fama da rashin wuta, amma TCN ya ce injiniyoyinsa na aiki tukuru don gyara wutar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng