Gwamna Ya Bude Tashoshin Mota domin Rage Raɗaɗi Tsadar Fetur
- Gwamnatin jihar Katsina karkashin Dikko Umaru radda ta bude tashoshin mota domin rage radadin tsadar rayuwa ga talakawa
- Mai girma Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da sayen motoci domin rage radadin cire tallafin mai
- Gwamnatin jihar Katsina ta kashe makudan kudi har Naira miliyan 50 wajen gina tashoshin da samar musu da abubuwan zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta gina tashoshin mota guda biyu domin saukaka harkar zirga zirga ga talakawa.
Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa dole ne a fito da dabarun saukakawa al'umma saboda halin da ake ciki.
Legit ta tatttaro bayanai kan yadda aka bude tashoshin ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bude tashoshin mota a Katsina
Gwamnatin Katsina ta bude tashoshin mota guda biyu a ƙananan hukumomi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Rahotanni na nuni da cewa an bude tashoshin ne a kananan hukumomin Mashi da kuma Ingawa na jihar Katsina.
Radda ya umarci shugabannin sufuri a tashoshin da su rika yin sauki ga matafiya domin rage musu raɗaɗin rayuwa.
Gwamna Radda zai saye karin motoci 40
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa zai saye karin motoci har 40 domin bunkasa harkar sufuri a Katsina.
Shugaban harkar sufuri a tashoshin Katsina, Haruna Musa Rugoji ya mika godiya ga gwamna Radda bisa kokarin da yake musu.
Nawa aka kashe wajen gina tashoshin?
Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa an kashe kudi har Naira miliyan 26 a Ingawa yayin da aka kashe Naira miliyan 24.6 a Mashi.
An samar da rijiyoyin zamani, ban-ɗakuna, masallaci, wuta mai amfani da hasken rana da wasu abubuwan more rayuwa a tashoshin.
Gwamna Radda zai karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina ta amince da kawo shirin sayar da abinci a farashi mai sauki a dukkan kananan hukumomin jihar.
Gwamna Dikko Umamar Radda ya tabbatar da cewa za a kafa shagunan ne domin sayar da abinci da ake amfani da shi a yau da kullum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng