Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Abin da Matarsa Ta Yi Lokacin da Yake Gidan Yari

Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Abin da Matarsa Ta Yi Lokacin da Yake Gidan Yari

  • Olusegun Obasanjo ya kara yabawa matarsa, Marigayiya Stella Obasanjo a wurin bikin ƙaddamar da asibitin da aka raɗawa sunanta
  • Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana yadda Stella ta shiga ta fita, ta karaɗe manyan ƙasashe a duniya domin a sako shi daga gidan yari
  • Obasanjo ya yi zaman gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha amma daga bisani ya fito kuma ya lashe zaɓen shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tuna irin wahalar da ya sha a gidan yari da kuma rawar da matarsa Stella ta taka wajen ganin an sako shi.

Cif Olusegun Obasanjo ya tuna baya ne a lokacin da yake jawabi a wurin buɗe sabon asibitin Stella Obasanjo mai gadaje 250 a Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban limami a Najeriya

Obasanjo.
Obasanjo ya fadi rawar da matarsa Stella ta taka don fito da shi daga Kurkuku Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Facebook

Yadda Marigayi Abacha ya ɗaure Obasanjo

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayi Sani Abacha ne ya kama Obasanjo tare da daure shi a gidan yari bisa zarginsa da yunkurin juyin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai gwamnatin soji ta AbdulSalam Abubakar ta sake shi bayan rasuwar Abacha kafin daga bisani ya samu nasarar zama shugaban kasa.

Marigayi Stella, wadda ita ma ‘yar asalin Edo ce, ta yi fice sosai a lokacin gwagwarmayar neman a saki Obasanjo.

Bayan Cif Obasonjo ya hau gadon mulki a 1999, Stella ce ta zama uwar gidan shugaban kasa watau 'First Lady' duk da cewa ba ita kaɗai ba ce matarsa.

Stella ta rasu ne a zango na biyu na mulkin tsohon shugaban ƙasa Obasanjo.

Obasanjo ya faɗi ƙoƙarin da Stella ta yi

Da yake ba da labarin abin da ya faru, Obasanjo ya yabawa marigayiya matarsa ​​wacce a cewarsa ba ta bar komai ba wajen ganin an sake shi daga gidan yari.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

A rahoton Vanguard, Obasanjo ya ce:

"Marigayiya matata ta shiga ta fita, ba inda ba ta je ba domin a sake ni daga kurkuku, ta je Faransa da birnin Vatican da wasu ƙasashen duniya, duk an faɗa mani bayan na fito.
"Muna shirin bikin cika shekaru 68 a duniya amma Allah bai nufa ba, ta mutu. Rasuwarta ta mani zafi da ni da dukkan iyalina. Ban san da me zan gode maku ba da kuka yi wannan don karrama ta."

"Ban nemi wa'adi na 3 ba" - Obasanjo

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya yi fatali da rade-radin da ake cewa ya nemi wa'adi na uku a karshen mulkinsa.

Obasanjo ya ce kwata-kwata a lokacin bai nemi hakan ba, ya ce idan yana so hakan ya fi komai saukin samu a gare shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262