Matasa Sun Taso da Batun Kudin N Power, Sun Aika Muhimmin Sako ga Sabon Minista
- Masu cin gajiyar N-Power da har yanzu ba a biya su haƙƙinsu ba sun rubuta ƙorafi zuwa ga sabon ministan jin kai, Nentawe Yilwatda
- Matasan waɗanda suka yi aiki a rukunin C II daga watan Oktoba, 2022 zuwa Satumba, 2023 sun buƙaci minista ya duba lamarinsu
- Sun bayyana cewa duk aikin da aka ɗora masu sun kammala amma har yanzu gwamnati ba ta biya su kuɗinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Matasa sun sake taso da batun biyan haƙkokin ƴan N-Power bayan sabon ministan harkokin jin ƙai da rage raɗaɗin talauci, Nentawe Yilwatda ya kama aiki.
Wasu daga cikin ƴan N-Power sun rubuta ƙorafi sun kai wa sabon ministan, suka roƙi a biyasu kuɗin aikin da suka yi daga watan Oktoba, 2022 zuwa Satumba, 2023.
Ƴan N-Power sun aika sako ga minista
Hakan na kunshe ne a wata takarda mai dauke da sa hannun lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, a madadin ƴan N-Power, Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar na ɗauke da kwanan ranar 5 ga Nuwamba, 2024, da taken, “Bukatar biyan haƙƙin ma’aikatan N-Power daga Oktoba 2022 zuwa Satumba 2023."
Yadda kuɗin N-Power suka maƙale
Idan baku manta ba ma'aikatan N-Power sun biyo gwamnatin tarayya bashin alawus dinsu na wata-wata har na tsawon shekara.
A baya tsohuwar ministar jin ƙai, Betta Edu, ta fara kokarin biyan bashin amma daga baya aka dakatar da ita bisa zargin hannu a karkatar da wasu kuɗaɗe.
A ƙorafin da masu cin gajiyar shirin N-Power suka aikawa sabon ministan jin ƙai, sun yi bayanin cewa sun sauke duk nauyun da aka ɗora masu amma haƙkinsu ya maƙale.
Ma'aikatan N-Power su bukaci a biya su haƙƙinsu
A takardar, lauyan ya ce:
"Matasan nan sun yi rijista kuma an ɗauke su aikin N-Power na wucin gadi, sannan aka tura su wurare daban-daban domin su yi aikin shekara guda daga Oktoba, 2022 zuwa Satumba, 2023.
"Duk da sun cika dukkan wajibai na aikin N-Power cikin amana ta hanyar ba da lokaci da ƙarfinsu, har yanzu ba a biya su hakkokinsu na wata-wata ba."
Ƴan N-Power sun nuna damuwa
A wani rahoton, an ji cewa matasa ƴan N-Power sun nuna damuwa da shirin gwamnatin tarayya na rusa ma'aikatar harkokin jin kai da yaƙi da fatara.
Shugaban N-Power na jihar Kano, Nazifi Mohammed Abubakar ya ce ma'aikatar ce kaɗai wata hukumar gwamnati mai alaka da talakawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng