"Za a Cigaba da Samun Matsalar Lantarki:" TCN Ya Fadi Lokacin Magance Rashin Wuta

"Za a Cigaba da Samun Matsalar Lantarki:" TCN Ya Fadi Lokacin Magance Rashin Wuta

  • Kamfanin rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) ya ce za a jima kafin wuta ta daidaita bayan yawan samun matsala
  • Manajar hulda da jama'a ta kamfanin, Ndidi Mbah ta sanar da haka, inda ta ce sai an kammala gyare-gyaren kafin a ga daidai
  • Zuwa yanzu, kamfanin ya gyara lantarkin Abuja da kewaye kuma ana gyaran sauran da ke sassan kasa bayan durkusewar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) ya ce za a cigaba da samun matsalar rashin wuta na tsawon lokaci.

Jawabin TCN na zuwa bayan wutar lantarki ta lalace sau 11 daga farkon shekarar 2024, an samu matsalar lantarki na baya bayan nan sau biyu a cikin kwanaki uku.

Kara karanta wannan

Lalacewar tashar wutar lantarki: Ƴan Najeriya sun fusata, sun kira Tinubu

Lantarki
TCN ya ce za a cigaba da samun matsalar lantarki Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Manajan darakta kan yada labaran TCN, Ndidi Mbah ta ce lalacewar wuta a kwanan nan ta faru saboda karuwar karfin wuta daga 50.33Hz zuwa 51.44Hz.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TCN ya ce ana gyaran wutar lantarki

Arise TV ya ruwaito cewa kamfanin TCN ya ce har yanzu ana cigaba da gyaran wutar lantarki da ke yawan samun matsala a sassan Najeriya.

Manajan hulda da jama'ar kamfanin, Ndidi Mbah ta ce tun bayan karfin wuta da aka samar ta lalace tashar wuta ne aka rufe wasu kananan tashoshi.

TCN ya fadi lokacin dawowar lantarki

Kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya ce tuni aka dawo da wutar lantarki yankin Abuja bayan lalacewar da ta yi a kwanan nan.

Ana kokarin gyara tashar lantarki da ke Shiroro-Mando, karamar tashar wuta a Jebba da kuma wanda ke Ugwuaji -Apir.

Kara karanta wannan

Ana fama da rashin wuta, kamfanonin lantarki sun kara kudin mita

TCN ya ce wutar lantarki ba za ta dawo kasar nan yadda ya dace ba har sai an kammala gyare-gyaren.

Kamfanin TCN ya yi bayani kan gyaran lantarki

A wani labarin kun ji cewa kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya yi karin haske a kan yadda gyaran wutar lantarki a Arewacin Najeriya ke gudana.

Kamfanin TCN ya bayyana cewa tun bayan da aka samu katsewar hasken wutar aka ta da Injiniyoyi domin tabbatar da an yi gyaran da zai dawo da lantarki yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit Hausa ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.