Lagbaja: Gwamna Ya Ayyana Kwanaki 3 domin Makokin Shugaban Soji
- Gwamnatin jihar Osun ta ayyana kwanaki uku domin zaman makoki bayan rasuwar shugaban sojojin kasan Najeriya
- Laftanal Janar Taoreed Lagbaja wanda dan asalin jihar Osun ne ya rasu bayan fama da jinya da ya yi yana dan shekaru 56 a duniya
- A ranar Laraba, 6 ga watan Nuwambar 2024 shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar shugaban sojojin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ayyana kwanaki uku domin zaman makokin shugaban sojojin ƙasan Najeriya.
Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa dukkan al'ummar jihar Osun suna baƙin ciki bisa rasuwar Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.
Jaridar Punch ta wallafa cewa daga yau Alhamis, 7 ga watan Nuwamba za a fara zaman makokin da gwamnan ya ayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar shugaban sojojin Najeriya
A ranar Laraba gwamnatin Najeriya ta sanar da rasuwar shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.
Laftanal Janar Lagbaja ya kasance dan asalin yankin Ilobu na jihar Osun kuma ya mutu ya bar mata daya da yara biyu.
Gwamantin Najeriya ta dakatar da shirye shirye da dama saboda mutuwar babban hafsun sojojin kasar a makon nan.
Lagbaja: Za a yi makokin kwanaki 3 a Osun
Pulse Nigerian ta wallafa cewa gwamnatin jihar Osun ta ayyana kwanaki uku domin zaman makoki bayan rasuwar Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.
Gwamna Ademola Adeleke ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Laftanal Janar Lagbaja da dukkan al'ummar jihar.
"Daga yau Alhamis, 7 ga Nuwamba za mu fara makokin rasuwar Laftanal Janar Lagbaja har zuwa ranar Asabar.
Za mu tanadi rajistar makoki a gidan gwamnati domin ba dukkan al'umma damar zuwa su isar da sakon ta'aziyyarsu."
- Ademola Adeleke, gwamnan Osun
Buhari ya yi ta'aziyyar shugaban sojoji
A wani rahoton, kun ji cewa bayan mutuwar hafsan sojoji, Janar Taoreed Lagbaja, tsohon shugaban kasa ya janatawa yan Najeriya kan rashin da aka yi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kadu da mutuwar Laftanal Janar Taoreed Lagbaja inda ya ce tabbas an yi babban rashi a kasar Najeriya baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng