DHQ: Dakarun Sojoji Sun Samu Babbar Nasara, Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 400

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Samu Babbar Nasara, Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 400

  • Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun sojoji sun tura ƴan ta'adda 481 lahira, sun ceto mutane 492 da aka yi garkuwa da su
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan ranar Alhamis, ya ce sojoji sun samu wannan nasara ne a wata guda
  • Buba ya ce zabi ɗaya ya rage wa ƴan ta'adda shi ne su miƙa wuya, idan kuma ba haka za su baƙunci lahira a hannun sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarori masu dumbin yawa a koƙarin wanzar da zaman lafiya a sassan Najeriya a watan Oktoba da ya gabata.

Gwarazan sojoji a rundunoni daban-daban sun hallaka ƴan ta'adda 481 tare da cafke wasu 741 da ake zargi da aikata miyagun laifuka a wata ɗaya kacal.

Kara karanta wannan

Sun sha wuta: Manyan yan bindiga sun fara neman mika wuya a ajiye makamai

Dakarun sojoji.
Sojojin Najeriya sun kashe yan ta'adda 481 a watan Oktoba Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ), Manjo Janar Esward Buba ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 492

Buba ya ce a wannan wata da ake magana a kansa na Oktoba, sojoji sun ceto mutane 492 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban.

Edward Buba ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato makamai 480 da alburusai 9,026, The Nation ta ruwaito.

Ya jaddada cewa ƴan ta'adda ba za su iya haɗa kansu da sojoji ba, yana mai ba su shawara su gaggauta ajiye makamai su tuba tun kafin su fuskancin fushin dakarun sojoji.

DHQ ta bai wa ƴan ta'adda zaɓin karshe

"Babu tantama ƴan ta'adda sun san ba su da ƙarfin sojoji, zaɓi ɗaya gare su, su ajiye makamai su miƙa wuya ko kuma mu tura su barzahu a filin yaƙi.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira, mutum sama da 20 sun rasu da iftila'i ya afka masu a jihohi 2

"A yanzu wasu kwamandoji da jagororin ƴan ta'adda sun nuna suna son ajiye makamai, za mu buɗe ƙofar miƙa wuya saboda wasu dalilai."

- Kakakin DHQ, Manjo Janar Buba.

Sojoji sun damke jagoran ƴan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke jagoran ƴan bindiga, Abubakar Ibrahim wanda ake kira da Habu Dogo a jihar Sakkwato.

Rundunar sojoji ta ce Habu Dogo na cikin shugabannin ƴan ta'adda da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo a Najeriya da Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262