Daga Gyarawa, Tushen Wutar Najeriya Ya Kara Lalacewa, Kasa ta Shiga Duhu

Daga Gyarawa, Tushen Wutar Najeriya Ya Kara Lalacewa, Kasa ta Shiga Duhu

  • Rahotanni na nuni da cewa tushen wutar Najeriya ya kara lalacewa karo na biyu a cikin tsawon kwanki uku
  • Lamarin ya jefa yan Najeriya a cikin duhu tare da tsayar da sana'o'i da harkokin yau da kullum ga al'umma
  • Injiniyoyin TCN sun dukufa gyara tushen wutar domin dawo da haske ga miliyoyin yan Najeriya a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yau Alhamis, 7 ga watan Nuwamba taushen wutar Najeriya ya sake lalacewa inda al'umma suka shiga duhu.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na biyu tushen wutar yana lalacewa a tsawon kwanaki uku.

Lantarki
Wutar Najeriya ta lalace. Hoto: Kola Sulaiman
Asali: Getty Images

Kamfanin rarraba wutar lantarki na JED ya sanar da lalacewar tushen wutar a shafinsa na Facebook tare da ba al'umma hakuri.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Abubuwan da suka jefa mutane cikin yunwa da mafitarsu a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tushen wutar Najeriya ya dauke

Hukumomi sun tabbatar da lalacewar tushen wutar lantarkin Najeriya a yau Alhamis da misalin karfe 11:30 na safe.

Lamarin ya faru alhali yan Najeriya ba su gama farfaɗowa daga lalacewar da ya yi ba a kwanaki biyu da suka wuce.

Kamfanonin raba wuta sun ba da hakuri

Tuni dai kamfanonin rarraba wutar lantarki na Najeriya suka fara ba mutane hakuri kan lamarin.

"Mun samu katsewar wutar lantarki a yau Alhamis, 7 ga watan Nuwamba da misalin karfe 11:29 na safe.
A yanzu haka ana ƙoƙarin warware matsalar domin dawo muku da wutar lantarki. Muna ba ku hakuri."

- Kamfanin EKEDC na Ikeja

"Katsewar wutar lantarki da aka samu a jihohin da muke aiki ya samo asali ne daga lalacewar taushen wuta na kasa.
Da zarar an kammala gyare-gyare za mu dawo muku da lantarki domin cigaba da ayyukan yau da kullum.

Kara karanta wannan

An fara dawo da wutar lantarki a yankuna, TCN ya bukaci a kwantar da hankali

Muna fata za ku cigaba da hakuri a kan lamarin kamar yadda kuka saba a baya. Mun gode."

- Kamfanin JED na Jos

An kara kudin mitar wuta a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanonin rarraba hasken lantarki da ake kira da DisCos sun kara daga farashin mita ga abokan huldarsu.

Wannan shi ne karo na biyu da kamfanonin su ka kara farashin a cikin watanni hudu, tun bayan kara kudi a watan Agusta da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng