Zanga Zanga: Gwamna a Arewa Ya Ba Yaran da Aka Sako Kyautar N100,000 da Manyan Wayoyi

Zanga Zanga: Gwamna a Arewa Ya Ba Yaran da Aka Sako Kyautar N100,000 da Manyan Wayoyi

  • Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani ya bai wa yaran Kaduna da aka sako kyautar N100,000 da manyan wayoyin hannu na zamani
  • Uba Sani ya kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafa masu a wurin taron miƙa kowane yaro ga iyayensa ko ƴan uwa a Kaduna
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta saki yaran waɗanda aka kama lokacin zanga-zanga bisa zargin cin amanar ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Kananan yaran Kaduna 39 da aka kama lokacin zanga-zanga a watan Agusta sun sake komawa cikin iyalansu.

Gwammatin Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta maida yaran hannun ƴan uwansu bayan kotu ta sake su bisa umarnin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya tarbi yara 39 da aka sako, ya gwangwaje su da kyaututtuka

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Gwamna Uba ya ba ƙananan yaran da aka sako N100,000 da manyan wayoyi Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da taron damƙa yaran hannun iyaye da ƴan uwansu ne a 'Gidan yara' da ke kan titin Kauru a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kaduna ya ba yaran tallafi

A taron dai Gwamna Uba Sani ya ba kowane yaro kyautar N100,000 da danƙareriyar wayar hannu Itel A18s a wani ɓangare na ƙoƙarin maido su cikin jama'a.

Gwamna Uba wanda sakataren gwamnatin jihar Kaduna Dr. Abdulkadir Muazu Meyere ya wakilta, ya tabbatarwa yaran cewa gwamnati za ta ci gaba tallafa masu.

Ya jaddada kudirin gwamnatin Kaduna na samar da hanyoyin samu da damarmaki ga yaran don taimaka musu su girma su zama masu bin doka da oda.

Uba Sani ya karɓi takarsun wasu

Abdulkadir Meyere ya ce gwamnan ya umarce shi da ya karbo takardun shaida daga wadanda suka kammala karatunsu na jami'a domin duba yiwuwar tallafa masu.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

Daga cikin tallafin da gwamnan ke shirin ba waɗanda suka gama karatu har da jari mai kauri da za su fara sana'a, koyar da sana'o'i ko ɗaukarsu aiki.

Ya kuma ce gwamnati za ta sanya ido kan kowane yaro, tare da bayar da karin taimako bisa la’akari da gwargwadon yadda suka shiryu suka zama ƴan ƙasa na gari.

Gwamnatin Uba Sani ta karɓi bayanan kowane yaro, kama daga adireshi, lambar waya, bayanan iyayensa ko na kusa da shi domin bibiyarsu.

Dalilin sakin yara masu zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa tausayi da jin kai ya sa Bola Tinubu ba da umarnin a saki yaran da aka tsare.

An ji cewa Tinubu a matsayinsa na uba ƙasa, ya bai wa yaran damar su shiryu su zama na kirki duk da akwai hujjoji a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262