Gwamna Zai Saye Abincin N3bn Ya Sayarwa Talakawa da Sauki

Gwamna Zai Saye Abincin N3bn Ya Sayarwa Talakawa da Sauki

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar da shiri na musamman domin karya farashin abinci
  • Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewa zai tabbatar da mutanen Bauchi ba su shiga ƙaranci da tsadar abinci ba
  • An ce shirin zai mayar da hankali wajen sayen abinci a lokacin da yake araha sai a sayar da shi da sauki idan ya yi tsada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da shiri na musamman domin karya farashin kayan abinci.

Gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewa zai cigaba da ƙoƙari har sai talakawa sun samu sauƙin rayuwa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a hedikwatar NNPCL, Mele Kyari ya shiga tsaka mai wuya

Bala Muhammad
Gwamnatin Bauchi za ta karya farashin abinci. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanai kan shirin ne a cikin wani sako da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin karya farashin kayan abinci a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da shirin sayen abinci a lokacin da ya yi sauki da sayar da shi da rahusa idan ya yi tsada.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamnan ya ware kudi har Naira biliyan uku domin sayen kayan abinci.

Mai girma gwamnan ya haɗa kwamiti na musamman da zai jagoranci shirin wajen sayen abinci da adana shi.

Kwamitin sauke farashin abinci a jihar Bauchi

Sanata Bala Mohammed ya naɗa Hon. Hamza Koshe Akuyam a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin karya farashin abinci.

Sarakunan Darazo da Gamawa, ma'aikatar noma da sauran manyan jami'an gwamnati na cikin yan kwamitin.

Gwamna ya gargaɗi kwamitin abinci

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya rage masu zaman kashe wando, zai dauki mutum 10,000 aiki

Sanata Bala Mohammed ya gargaɗi kwamitin da cewa dole su tabbatar da sun yi aiki tare da bayyana komai kamar yadda yake faruwa ba tare da ha'inci ba.

Gwamnan ya ce yana fatan shirin zai zamo sanadin samun sauƙin farashin kayan abinci a jihar Bauchi.

Za a karya farashin abinci a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina ta amince da kawo shirin sayar da abinci a farashi mai sauki a dukkan kananan hukumomin jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya tabbatar da cewa za a kafa shangunan ne domin sayar da abinci da ake amfani da shi a yau da kullum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng