'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Limami a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Limami a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun yi ta'asa bayan sun sace wani limamin cocin Katolika a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Miyagun sun sace limamin cocin ne a yammacin ranar Talata lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa cocinsa bayan ya je aiki
  • Cocin ya tabbatar da sace limamin, ta buƙaci a saka shi a addu'a domin ya samu ya kuɓuta daga hannun waɗanda suka sace shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Rev. Fr. Emmanuel Azubuike, limamin cocin St. Theresa’s Catholic Parish a yankin Obollo, ƙaramar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun yi garkuwa da limamin cocin ne a kusa da ƙauyen Aliyi da ke yankin Obollo a lokacin da yake komawa cocinsa bayan ya je wani aiki.

Kara karanta wannan

Malami ya yi abin kunya, kotu ya yanke masa hukunci kan lalata da mace a Masallaci

'Yan bindiga sun sace limamin coci a Imo
'Yan sun yi garkuwa da limamin coci a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, cocin Katolika ta Okigwe ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace limamin coci

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren cocin, Rev. Fr. Princewill Iwuanyanwu, ta buƙaci a yi addu'o'i domin kare lafiyar limamin da kuma fatan dawowarsa lafiya, rahoton The Punch ya tabbatar.

"An umurce ni da na sanar da ku cewa ɗaya daga cikin limamanmu, Rev. Fr. Emmanuel Azubuike, an yi garkuwa da shi a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba, 2024, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma."
"An yi garkuwa da shi ne a kusa da ƙauyen Aliyi a Obollo, a ƙaramar hukumar Isiala Mbano, jihar Imo yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga wani aiki."
"Muna roƙon addu'o'in ku domin dawowarsa cikin ƙoshin lafiya."

Kara karanta wannan

"Cin mutunci ce": Jagora a PDP ya soki tsare yara saboda zanga zanga

- Rev. Fr. Princewill Iwuanyanwu

An fara addu'ar neman kuɓutar limamin kirista

A halin da ake ciki, kansilan yankin Obollo, David Ajaero, ya tabbatar da yin garkuwa da limamin cocin, ya ce mutanen yankin sun fara addu’ar neman kuɓutarsa.

Ajaero wanda ya bayyana limamin a matsayin mutumin kirki, ya yi kira da a gaggauta sakinsa.

Ƴan sanda sun sheƙe masu garkuwa da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce jami’anta sun samu nasara kan masu garkuwa da mutane a jihar.

Rundunar ƴan sandan ta ce jami'anta sun kashe wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng