Gwamna Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Shugaban Alkalai Awanni bayan Rasuwa

Gwamna Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Shugaban Alkalai Awanni bayan Rasuwa

  • Gwamna Biodun Oyebanji ya naɗa sabon shugaban alkalai na riko a jihar Ekiti bayan rasuwar Mai Shari'a John Oyewole
  • Mai ba gwamna shawara kan harkokin midiya, Yinka Oyebode shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa, ya ce naɗin zai fara aiki nan take
  • Tsohon shugaban alkalan, Oyewole ya rasu ne ranar 4 ga watan Nuwamba bayan fama da jinya ta tsawon watanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Biodun Oyebanji, ya nada Mai shari’a Lekan Adekanye Ogunmoye a matsayin mukaddashin shugaban alkalan jihar.

Gwamnan ya yi wannan naɗi ne kamar yadda sashi na 271 (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ya tanada.

Kara karanta wannan

Babban alkali a Najeriya da ginin kotu ya rufta kansa ya rasu yana da shekaru 64

Gwamnan Ekiti, Oyebanji.
Gwamna Oyebanji ya nada sabon mukaddashin shugaban alkalai a jihar Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sabon shugaban alkalan jihar Ekiti zai fara aiki ne daga ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban alkalan Ekiti ya rasu

Lekan Adekanye ya maye gurbin tsohon shugaɓan alkalan jihar Ekiti, Mai Shari'a John Oyewole Adeyeye, wanda ya rasu a ranar 4 ga Nuwamba, 2024.

Mai shari’a Oyewole ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya tsawon wata da watanni.

Taƙaitaccen bayani kan Mai Shari'a Ogunmoye

An haifi sabon muƙaddashin shugaban alkalan jihar Ekiti, Mai Shari'a Lekan Ogunmoye a ranar 6 ga watan Nuwamba, 1963, The Nation ta ruwaito.

Hakan na nufin a yau Laraba alkalin yake cika shekaru 71 da haihuwa, ga shi kuma mai grima gwamna ya naɗa shi shugabanci.

Mai shari'a Ogunmoye ya zama cikakken lauya a Najeriya a shekarar 1987 kuma an naɗa shi a matsayin alkalin kotu a ranar 1 ga watan Afrilu, 2010.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu

Mista Yinka Oyebode, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce Oyebanji ya yi wa sabon mukaddashin shugaban alkalan fatan nasara.

Gwamna Iyebanji ya ba ma'aikata kyauta

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji ya mikawa ma’aikata 82 kyautar tsabar kudi Naira miliyan 42 saboda kwazon da suka nuna a aiki.

A yayin wani taron kungiyar ma’aikatan gwamnati, Oyebanji ya yi wa ma’aikata alkawarin biyan sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262