Buhari Ya Kai Ziyara, Ya ba Talakawa Tallafin Miliyoyi bayan Haɗarin Jigawa
- Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Jigawa domin jaje bayan hadarin tankar man fetur da aka yi a garin Majia
- Muhammadu Buhari ya yi jaje ga al'ummar jihar bisa hadarin da ya laƙume rayuka sama da 200 kuma ya bayar da tallafin miliyoyi
- Shugaba Buhari ya samu rakiyar ministocin gwamnatinsa da suka hada da Sheikh Isa Ali Pantami, Hadi Sirika da wasu manyan jami'ai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Jigawa bayan hadarin tankar man fetur.
A watan da ya wuce aka samu hadarin tankar mai da ya laƙume rayuka sama da 200 a garin Majia na karamar hukumar Taura.
Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar Buhari ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Umar Namadi, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Buhari ya je jaje a jihar Jigawa
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Jigawa domin jaje kan hadarin tankar mai da ya faru a watan Oktoba da ya wuce.
Mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman Gumel ne ya karbi Buhari da tawagarsa yayin ziyarar.
Buhari ya ba da tallafin Naira miliyan 10
Bayan ta'aziyya da jaje, shugaba Buhari ya mika tallafin kudi Naira miliyan 10 ga gwamnatin jihar Jigawa.
Za a yi amfani da tallafin kudin ne domin ba iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunuka yayin haɗarin.
Mutanen da suka raka Buhari zuwa Jigawa
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami na cikin waɗanda suka raka Buhari jihar Jigawa.
Haka zalika sakataren gwamnatin Buhari, Boss Mustapha, tsohon ministan sufuri, Hadi Sirika na cikin waɗanda suka taka masa baya.
Buhari ya yi addu'ar samun rahama ga wadanda suka rasu da kuma samun sauki ga waɗanda suka jikkata.
Buhari ya ziyarci jihar Borno
A wani rahoton, Legit ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Borno bayan dawowarsa daga kasar waje.
Muhammadu Buhari ya ziyarci Borno ne domin jaje ga al'ummar jihar bayan mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a jihar a watan Satumba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari
Asali: Legit.ng