"Ba Gyaran Tarbiyya ba": Ndume Ya Fadi Abin da Ya Dace a Yi Wa Yaran da Aka Tsare
- Sanata Ali Ndume ya taɓo batun sakin yaran da aka saki bayan an tsare su saboda zargin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance
- Ndume ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta biya su ɗiyya kan abin da aka yi musu saboda an zalunce su
- Ya yi nuni da cewa diyya ita ce abin da ya fi dacewa da yaran ba wai a kai su wurin da za a yi musu gyaran tarbiyya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana ra'ayinsa kan sakin yaran da aka tsare saboda zanga-zanga.
Yaran dai an tsare su ne tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa zarginsu da shiga zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta.
Me Ndume ya ce kan yaran da aka tsare
A wata hira da gidan talabijin na Channels tv, Ndume ya bayyana cewa yaran da aka tsare kamata ya yi a ba su diyya ba wai a yi musu gyaran tarbiyya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya bayyana hakan ne biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya ba da na a saki dukkanin ƙananan yaran tare da yi musu gyaran tarbiyya.
"Bai kamata a ce an cafke waɗannan ƙananan yaran ba. Ba maganar gyaran tarbiyarsu ake yi a yanzu ba. Magana ce ta a biya su diyya, domin an zalunce su."
"An tauye musu haƙƙinsu. Ina ganin akwai buƙatar gwamnati ta ba su haƙuri sannan ta biya su diyya domin su fara rayuwarsu."
"Wannan shi ne abin da ya dace, ba wai a kai su wani wuri a ce ana son a yi musu gyaran tarbiyya ba."
- Sanata Ali Ndume
Sanatan ya ƙara da cewa bai kamata Tinubu wanda ya yi fafutukar kafa dimokuraɗiyya, ya shige kan gaba wajen salon mulkin da ƴan Najeriya ba za su amince da shi ba.
Dalilin sakin yaran da aka tsare
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin kananan yaran da aka kama saboda tausayi.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin yaran a fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2024.
Asali: Legit.ng