Fadan Daba Ya Jawo Sanadiyyar Rasa Rayukan Mutane a Benue
- Fadan daba tsakanin wasu ƙungiyoyin asiri ya jawo asarar rayuka a birnin Makurdi na jihar Benue a Arewa ta Tsakiya
- Hargitsin da aka samu tsakanin ƙungiyoyin guda biyu ya jawo sanadiyyar hallaka aƙalla mutane huɗu da asarar dukiya
- Mutanen yankin sun buƙaci gwamnati da ta kai musu ɗauki domin ka da a ci gaba da salwantar da rayukan bayin Allah haka nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - An samu asarar rayukan aƙalla mutane huɗu a wani faɗan daba na ƴan ƙungiyar asiri a jihar Benue.
Faɗan daban dai ya auku ne a unguwar North Bank da ke wajen birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa ƴan daban da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne na yin faɗan ne domin nuna ƙarfin iko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda faɗan daban ya ta'azzara
Majiyoyin sun bayyana cewa aƙalla mutane huɗu ne aka hallaka sakamakon rikicin a cikin sati ɗaya.
An kuma tattaro cewa an ƙona wani gida a yammacin ranar Talata, yayin da faɗan ke ci gaba da ƙamari.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƙungiyoyin waɗanda ake kira da 'Black' da 'Red' sun mayar da unguwar North Bank wani filin yaƙi wanda hakan ya sanya mutane tserewa daga wajen.
"Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki, idan ba haka ba waɗannan ƴan ƙungiyar asirin za su kashe mutane masu yawa."
"An yi wani kisa a jiya (Litinin) kuma har a yau (Talata) mun jiyo ƙarar harbe-harben bindiga."
- Wata majiya
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Ƙoƙarin jin ta bakin jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, bai haifar da ɗa mai ido ba.
Kakakin ƴan sandan ba ta ɗauki kiran da aka yi mata a waya ba sannan ba ta dawo da amsar saƙon da aka tura mata ta waya ba."
Ƴan daba sun tayar da hargitsi a Kano
A baya mun kawo muku rahoton cewa wasu fusatattun ƴan daba sun tayar da hargitsi a kasuwar filin masallacin idi da ke cikin birnin jihar Kano.
Hakan ya biyo bayan wa'adin sa'o'i 48 da gwamnatin jihar Kano ta bai wa ƴan kasuwar su tattara kayansu su tashi daga filin.
Asali: Legit.ng