Kotu Ta Ba da Umarni kan Hana ba Kananan Hukumomin Kano Kudi

Kotu Ta Ba da Umarni kan Hana ba Kananan Hukumomin Kano Kudi

  • Babbar kotun jihar Kano ta ba da umarni kan yiwuwar hana ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗe daga asusun tarayya
  • Kotun ta hana Akanta Janar na tarayya, bankin CBN da hukumar RMAFC hana ba ƙananan hukumomin Kano kuɗade duk wata
  • Wasu mambobin ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi (NULGE) suka shigar da ƙarar a gaban kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Musa Muhammad, ta ba da umarni kan riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar Kano.

Kotun ta bayar da umarnin hana hukumomin gwamnatin tarayya yin katsalanda ga kuɗaɗen da ake ba ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano duk wata.

Kotu ta hana rike kudaden kananan hukumomin Kano
Kotu ta umarci ka da a rike kudaden kananan hukumomin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa hukuncin kotun ya biyo bayan ƙarar da mambobin ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE) suka shigar a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gayawa gwamnatin Tinubu gaskiya kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane umarni kotun ta ba da?

A cikin umarnin kotun mai ɗauke da kwanan watan 4 ga watan Nuwamba, mai shari’a Ibrahim Musa ya ba masu shigar da ƙarar izinin miƙa takardun kotu a ofisoshin Akanta Janar na tarayya, bankin CBN da hukumar RMAFC.

Ƙarar wacce Bashir Yusif Muhammad Esq da Umar Bala Salisu Esq suka shigar, sun nuna damuwa kan yiwuwar riƙewa ko jinkirin ba da kuɗaɗen ƙananan hukumomin a jihar.

Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana hukumomin gwamnatin tarayya daga ɗaukar matakan da za su iya kawo cikas ga biyan kuɗaɗen da ake ba ƙananan hukumomin jihar Kano duk wata.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba, 2024, lokacin da za a ci gaba da sauraronta.

Kotu ta hana ba Rivers kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan ƙarar neman hana gwamnatin tarayya sakarwa gwamnatin jihar Rivers kuɗinta.

Kotun a hukuncin da ta yanke ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba ta hana gwamnatin tarayya daga ci gaba da sakarwa jihar Rivers kuɗaɗe duk wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng