Karancin Abinci: Abubuwan da Suka Jefa Mutane cikin Yunwa da Mafitarsu a Najeriya

Karancin Abinci: Abubuwan da Suka Jefa Mutane cikin Yunwa da Mafitarsu a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ƙarancin abinci na ɗaya daga cikin kalubalen da Najeriya ke fuskanta duk da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke ikirarin tana yi domin kawar da matsalar.

Ƙungiyar abinci da noma FAO ta majalisar dinkin duniya ta gudanar da bincike mai zurfi kan ƙarancin abinci da kuma lalubo mafita ga ƙasashen duniya.

Bola Tinubu.
Kunguyar FOA ta lissafa matsalolin da suka kawo karancin abinci da mafita a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Getty Images

A rahoton binciken wanda shafin FightFoodCrises ya wallafa, kungiyar ta hango tushen matsalar yunwa da ta addabi Najeriya da kuma hanyoyin da ya kamata a bi a magance su.

A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da kungiyar FOA ta majalisar dinkin duniya ta hango da kuma matakin da da kamata a ɗauka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban limami a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tushen ƙarancin abinci a Najeriya

Koma bayan tattalin arziki, ambaliyar ruwa, rikici, matsalar tsaro na cikin abubuwan da bincike ya nuna sun taka rawa wajen rashin wadatar abinci a Najeriya.

Rashin tsaro ya ƙara muni, tashe-tashen hankula sun karu da kashi 26 cikin 100 a Najeriya daga watan Janairu zuwa Agustan 2024 idan aka kwatanta da na 2023.

Adadin ƴan gudun hijira na ci gaba da ƙaruwa sakamakon hare-haren ƴan ta'adda, ƙididdiga ta nuna mutum akalla miliyan 3.6 ne suka bar gidajensu.

Kungiyar FAO ta ce waɗannan da ma wasu ƙalubale na rashin tsaro, su ne suka zama alaƙaƙai musamman a Arewa, har ta kai ga manoma ba su iya zuwa gonakinsu.

Matsalar tsaro ta ƙara ta'azzara

Haka zalika bayan ruwa ya ɗauke an samu ƙaruwar ayyukan ƴan fashin jeji da rikicin kabilanci a watan Oktoba, wanda ya samo asali ne daga matsin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci 7 a Abuja, bayanai sun fito

Ayyukan jin ƙai ba su kai wa ga mutanen da ya kamata a kauyukan Arewa, ma su ba da agaji sun taƙaita aikinsa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Ƙungiyar FAO ta ce wannan ya ƙara jefa mutanen da ke rayuwa a yankunan da babu tsaro cikin mawuyacin hali saboda rashin isar kayan tallafi da jin ƙai.

Hauhawar farashin kayayyakin da ba a taɓa gani ba

Sannan kuma ga hauhawar farashin kayayyaki wanda FAO ta ce ya yi tashin da ba a taɓa gani ba tsawon shekara 28 a Najeriya, ya kai kashi 32.2%.

A cewar rahoton, farashin kayayyakin abinci na amfanin yau da kullum ya nunka akalla sau biyu daga farkon shekara zuwa watan Yulin, 2024.

Ana hasashen lalacewar darajar Naira, karancin mai da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, da raguwar amfanin da ake nomawa a gona ka iya sake ɗaga farashin kaya a nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi kokarin da Tinubu ke yi domin rage tsadar rayuwa a Najeriya

Ƴan Najeriya miliyan 31 8 na iya faɗawa matsala

Binciken ya nuna cewa kusan ƴan Najeriya miliyan 31.8 ake hasashen za su fuskanci yunwa mai muni sabida rashin abinci a lokacin bazara.

Wannan yana nuna an samu karuwar kashi 3 cikin 100 na adadin mutanen da ke fama da rashin wadataccen abinci idan aka kwatanta da daidai lokacin a bara 2023.

Shawarwarin matakan da ya kamata a ɗauka

1. Ba da tallafin tsabar kudi, kayan abinci da dukkan nau'ikan kayan amfanin yau da kullum ga mazauna yankunan da lamarin tsaro ya yi muni.

Haka kuma ya kamata a tallafawa magidanta waɗanda ba su iya sayen abinci saboda tashin farashi a yankunan karkara da birane.

2. Bunƙasa harkokin noma ta hanyar samar da kayan aiki ga manoma da wadataccen ruwan da za a yi noman rani.

Hakan zai taimaka wajen samar da isasshen abinci da kuɗin shiga.

3. Samar da tallafin abinci mai gina jiki ga rukunin mutane masu rauni kamar ƙananan yara, mata masu juna biyu ko masu shayarwa, ƴan gudun hijira da masu masaukinsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya

Gwamnatin Tinubu ta kafe kan tsare-tsarenta

A wani rahoton, kun ji cewa ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya karbi baƙuncin sabuwar karamar ministar da Bola Tinubu ya naɗa a ma'aikatarsa

Edun ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun cire tallafin man fetur da tsame hannun gwamnati a harkar farashin kudin ketare

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262