Gwamnati Ta Sauya Tsarin Shekarun Shiga Jami'a Kwana 1 da Nada Minista

Gwamnati Ta Sauya Tsarin Shekarun Shiga Jami'a Kwana 1 da Nada Minista

  • Gwamnatin tarayya ta sauya matsaya kan maida shekarun shiga manyan makarantu zuwa shekara 18 a ƙasar nan
  • Sabon ministan ilmi, Dr. Morufu Olatunji Alausa ne ya sanar da sauya tsarin a ranar Talata, 5 ga watan Agustan 2024
  • Ministan ya bayyana cewa tsarin yana da illa ga ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na rage yawan yaran da ba su makaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan ilmi, Dr. Morufu Olatunji Alausa, ya sauya tsarin da magabacinsa ya fito da shi na ƙayyade shekara 18 a matsayin shekarun shiga jami'a.

Tsarin wanda tsohon ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman, ya ɓullo da shi ya haifar da cece-kuce.

Gwamnatin Tinubu ta sauya tsarin kayyade shekarun shiga jami'a
Gwamnatin tarayya ta canza tsarin kayyade shekarun shiga jami'a Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ministan ilmin ya sanar da sauya tsarin ne yayin da yake yi wa manema labarai bayan ya fara aiki a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan yaran da aka tsare saboda zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Tinubu ta sauya tsarin

Dr. Olatunji Alausa ya ce tsarin ya yi illa ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya ke yi rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan.

Ministan ya ce tsarin ba abin da haifar da ɗa mai ido ga ɓangaren ilmi, inda ya ce za a ci gaba da amfani shekara 16 a matsayin shekarun shiga jami'a.

Sabon ministan ya kuma bayyana cewa daga yanzu tsarin ilmin Najeriya zai koma kaso 80% a aikace sannan kaso 20% a takarda.

Ya nuna tsarin karatu a aikace zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi.

Ya makomar masu digirin bogi?

Olatunji Alausa ya bayyana cewa ba za a sauya matakin soke digirin bogi sama da 22,700 da gwamnatin tarayya ta yi waɗanda aka samo su a wasu jami'o'in ƙarya da ke ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya yi rashin hadimi, wani ɗan sanda ya rasu

Tunji Alausa na cikin ministoci 10 da suka samu sababin ma'aikata bayan da aka yi wa majalisar ministocin Shugaba Tinubu garambawul a watan da ya gabata.

Gwamnati ta magantu kan shekarun jarabawar sakandire

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi ƙarin haske kan batun mafi ƙarancin shekarun zana jarabawar gama sakandire a Najeriya.

Rahotanni sun yi iƙirarin cewa gwamnatin ta yanke cewa dole sai ɗalibi ya kai shekaru 18 gabanin a ba shi damar zana jarabawar WAEC da NECO.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng