An Fara Dawo da Wutar Lantarki a Yankuna, TCN Ya Bukaci a Kwantar da Hankali
- Kamfanin rarraba wuta na kasa, TCN ya bayyana cewa an fara dawo da wuta bayan lalacewar tushen lantarki na kasa a dazu
- TCN ya ce tun lalacewar tushen wutar injiniyoyi suka dukufa aiki domin ganin lamarin bai shafi harkokin yau da kullum na al'umma ba
- Legit ta tattauna da mutane a jihohi domin jin ko lantarki ta dawo a yankunansu kamar yadda TCN ta yi alkawari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa ya fara shawo kan matsalar lantarki da aka samu a yau.
TCN ya tabbatar da cewa a yanzu haka wutar ta fara dawowa a yankunan da suka samu matsala a Najeriya.
Kamfanin TCN ya bayyana nasarar da ya samu ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Talata, 5 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dawo da wutar lantarki a Abuja
Kamfanin TCN ya bayyana cewa an fara dawo da lantarki a wuraren da aka samu matsala bayan lalacewar tushen wuta na kasa.
TCN ya tabbatar da cewa wuta ta dawo a birnin tarayya Abuja kuma sannu a hankali sauran jihohi za su samu hasken lantarki.
Kamfanin ya kara da cewa matsalar da aka samu ba babba ba ce kasancewar wani sashe na tushen wutar bai samu matsala ba.
Jawabin TCN bayan daukewar wuta
"An samu matsalar lantarki da misalin karfe 1:52 na ranar yau, 5 ga watan Nuwamba.
A halin yanzu an dawo da wutar lantarki a birnin tarayya Abuja da misalin karfe 2:49 na rana.
Sannu a hankali dukkan sauran jihohi za su samu wutar da zarar an kammala gyare-gyare."
- TCN
A karshe, kamfanin TCN ya ba yan Najeriya masu amfani da lantarki hakuri kan lalacewar tushen wutar.
Wuta ta dawo a Gombe da Bauchi
Wani mazaunin Gombe, Naziru Nasiru ya zantawa Legit cewa wutar lantarki ta dawo cikin daren ranar Talata a jihar Gombe.
Haka zalika wani mazaunin Bauchi, Abbas Sa'idu ya tabbatar da cewa wutar da dawo kuma sun yi farin ciki da hakan.
Za a samar da wuta da hasken rana a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Gombe ta dauko aikin da zai kawo karshen matsalar wutar lantarki a jihar.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai yi aiki da kamfanin China domin samar da tashar lantarki mai amfani da hasken rana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng