Malami Ya Yi Abin Kunya, Kotu Ta Yanke Masa Hukunci kan Lalata da Mace a Masallaci
- Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai kan wani Malamin Musulunci, Alani Rafiu bayan kama shi da laifin kwanciya da ƙaramar yarinya
- An kama malamin ne bisa lalata rayuwar yarinya ƴar shekara 14 a cikin masallaci a yankin Ikotun a jihar Legas
- Mai shari'a Rahman Oshodi ya ce wanda ake zargin ya ci amanar da aka ba shi na kula da yarinyar da ba ta ilimi a matsayinsa na Malami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas - Wata kotun laifuffukan keta haddi da rikicin ma'aurata ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan wani Malamin da aka kama da yin lalata da mace a Masallaci.
Kotun mai zama a Ikeja ta ɗaure malamin watau Alfa, Alani Rafiu har karshen rayuwarsa kan laifin saduwa da ƴar shekara 14 bisa tilas kuma a ɗakin Allah.
Punch ta tattaro cewa Mai shari’a Rahman Oshodi ya yanke hukuncin ne a ranar Litinin bayan samun Rafiu da laifin lalata rayuwar ƙaramar yarinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda malamin ya aikata abin kunya
Tun farko dai an gurfanar da Malam Rafiu a gaban kotu a ranar 28 ga Oktoba, 2021, bisa tuhumar yin jima'i da ƙaramar yarinya a cikin Masallaci.
Lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Agusta, 2021, a yankin Ikotun a jihar Legas amma bayan gurfanar da shi, malamin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa.
Wannan ya sa aka fara shari'ar, inda masu shigar da kara karkashin jagorancin B. Boye, suka gabatar da shaidu uku ciki har da yarinyar da aka lalatawa rayuwa.
Kotu ta yankewa malamin hukunci dauri
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya ce lauyan masu kara ya yi aikinsa na gamsar da kotu cewa wanda ake tuhumar ya yi lalata da ƙaramar yarinyar.
Mai Shari'a Rahman ya ce ba za a iya kwatanta girman laifin da malamin ya aikata ba domin ya ci amanar da aka ba shi a matsayin malamin addini.
"Maimakon ka kare yarinya yar shekara 14 da aka damƙa a hannunka, ka koma kana lalata da ita a wurin ibada."
"Don haka, kotu ta yanke muka hukuncin daurin rai da rai kamar yadda sashe na 137 na dokar laifuka ya kunsa," in ji shi.
Ana zargin tsohon minista da ɗirkawa wata ciki
A wani labarin, an ji cewa wata kotu a Abuja ta yi zama kan zargin tsohon Minista a Najeriya da dirkawa wata budurwa ciki.
Ana zargin Kabiru Tanimu da yaudarar wata mai suna Hadiza na tsawon shekaru wanda har ta samu sami juna biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng