Za a Zaƙulo Yan Sandan da Suka 'Azabtar' da Yara Masu Zanga Zanga Inji IGP
- Sufeton yan sandan Najeriya ya tabbatar da cewa za su yi cikakken bincike domin zakulo wadanda suka azabtar da yaran zanga zanga
- IGP Kayode Egbetokun ya ce dole za a yi bincike domin tabbatar da gano gaskiyar abin da ya faru bayan kulle yaran da suka yi zanga zanga
- Matakin da yan sanda suka dauka ya biyo bayan umarnin da Bola Tinubu ya bayar ne na sakin yaran da aka gurfanar a ranar Jumu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya za ta gudanar da bincike kan jami'an da suka kulle yara masu zanga zanga a caji ofis.
Hakan na zuwa ne bayan an azabtar da yaran da aka kama da zargin kifar da gwamnatin Bola Tinubu yayin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.
Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafa kwamitin binciken 'yan zanga zanga
Tun a ranar 1 ga watan Nuwamba rundunar yan sandan Najeriya ta kafa kwamitin bincike kan halin da yaran zanga zanga suka shiga.
Lamarin ya biyo bayan gurfanar da yaran zanga zanga ne a cikin wani yanayi maras kyau wanda hakan ya jawo suka ga yan sanda da gwamnati.
Za a yi adalci bayan karbar rahoton kwamiti
Sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya ce sun samu rahoto daga kwamitin da suka kafa domin bincike kan lamarin.
IGP Kayode Egbetokun ya ce zai tabbatar da ya yi adalci bayan karɓar rahoton kwamitin tare da gyara kurakuran da aka samu.
Sufetan 'yan sandan ya bayyana cewa za su tabbatar da samar tsarin kulawa mai kyau ga yara ƙanana da ake bincike.
Yaushe za a fara binciken yan sanda?
Kayode Egbetokun ya ce ya gayyaci dukkan masu lura da wuraren da ake kulle masu laifi zuwa taro na musamman a ranar 7 ga watan Nuwamba.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa za ta cigaba da ƙoƙarin yin adalci a Najeriya musamman ga masu rauni.
Bayanin lauya yaran da aka kama a zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa lauya mai kare yaran da aka kama a lokacin zanga zangar tsadar rayuwa, Hamza Nuhu Dantani ya yi karin haske.
Barista Nuhu Hamza Dantani ya yi zargin cewa ba a bi ƙa'ida wajen kama yaran ba kuma an karya doka wajen gabatar da su a kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng