Jami'an EFCC Sun Cafke Abokin Takarar Atiku kan Badakalar N1.3trn
- Jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya sun cafke tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa
- An cafke Ifeanyi Okowa ne a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba kan zargin karkatar da N1.3trn lokacin ya na gwamna
- Okowa ya shiga hannu bayan ya kai kansa ofishin hukumar EFCC da ke Fatakwal domin amsa gayyatar da aka yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Jami’an hukumar yaƙi da yi wa masu tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) sun cafke tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Jami'an EFCC sun cafke Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da Naira Tiriliyan 1.3 na jihar Delta da aka aiko daga asusun tarayya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Wata majiya daga EFCC ta tabbatar da kama tsohon gwamnan ga tashar talabijin ta Channels tv a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama Okowa ne a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba, 2024, a birnin Fatakwal, jihar Rivers, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Meyasa EFCC ta cafke Ifeanyi Okowa?
Jami'an na EFCC sun cafke Okowa ne lokacin da ya kai kansa ofishin hukumar EFCC na Port Harcourt bisa gayyatar da aka yi masa.
Ana zargin tsohon gwamnan da gaza ba da ba'asi kan kuɗin da kuma wasu Naira biliyan 40 da ya yi ikirarin cewa ya yi amfani da su wajen siyan hannun jari a kamfanin UTM Floating Liquefied Natural Gas.
Ana zargin Okowa ya sayi hannun jari na Naira biliyan 40 a ɗaya daga cikin manyan bankunan ƙasar nan.
Haka kuma masu binciken suna bincikar karkatar da kuɗaɗen da tsohon gwamnan ya yi domin mallakar wasu gidaje a Abuja da birnin Asaba na jihar Delta.
Alakar Okowa da Atiku Abubakar
Okowa ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023.
Ana tsare da shi ne a wurin da EFCC ke tsare mutane a Fatakwal jihar Rivers.
Hukumar EFCC ta cafke Akanta Janar
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi watau EFCC ta cafke Akanta Janar na jihar Edo, Mr. Julius O. Anelu da wasu manyan jami'ai huɗu.
Bayanai sun nuna cewa EFCC ta tsare jami'an ne domin hana cire kuɗi daga lalitar gwamnatin Edo biyo bayan wani kasafi da ake zargin majalisar dokoki ta amince da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng