Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Rashin Hadimi, Wani Ɗan Sanda Ya Rasu
- Kofur Barde Nuhu, ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke aiki a ayarin mataimakin shugaban majalisar dattawa ya rasu
- Sanata Barau I. Jibrin ya ce ɗan sandan ya rasu ne a hanyar zuwa gida ganin iyalinsa a karamar hukumar Bosso ta jihar Neja
- Barau ya tura tawaga har gidansu ɗan sandan domin yi masu ta'aziyyar wannan rashi, ya roki Allah ya sa shi a gidan Aljannah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke aiki a tawagar mataimaikin shugaban majalisar dattawa, Kofur Barde Nuhu ya riga mu gidan gaskiya.
Barde Nuhu ya rasu ne a ranar Asabar a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar zuwa garinsu kauyen Shata da ke karamar hukumar Bosso a jihar Neja.
Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar Kofur Nuhu a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X jiya Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban majalisa ya yi ta'aziyya
Mataimakin shugaban majalisar ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin jajirtacce kuma mai himma a bakin aikinsa.
"Cikin raunin zuciya da miƙa al'amura ga Allah SWT, ina ta'aziyyar rasuwar CPS Barde Nuhu, wanda ya mutu a haɗarin mota a hanyar zuwa ganin iyalinsa a ƙaramar hukumar Bosso a jihar Neja.
"Kofur Barde dan sanda ne abin koyi, wanda ke gudanar da aikinsa cikin kwazo da amana. Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan aikinsa a rundunar 'yan sandan Najeriya.
"Allah SWT ya saka masa da Jannatul Firdausi, ya kuma kyautata makwancinsa kuma ya ba iyalansa haƙuri.
- Barau I. Jibrin.
A jiya Lahadi, Sanata Barau ya tura tawaga ta musamman zuwa mahaifar ɗan sanda a ƙaramar hukumar Bosso domin yi wa iyalansa ta'aziyyar rashin da suka yi.
Shugaban ƙaramar hukuma ya rasu a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar karamar hukumar Onigbongbo a Lagos sun shiga jimami bayan rasuwar shugabansu a ƙarshen makon da ya shige.
Marigayi ciyaman na ƙaramar hukumar, Oladotun Olakanle ya rasu ne da safiyar ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024 a jihar Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng